Zaban Kananan Hukumomi: Akwai Kuskuran Da Aka Tabka Shi Yasa Ba a Gayyace Mu Ba – Majigiri
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Katsina ta bayyana cewa akwai kurakuran da hukumar zabe mai zaman kanta ta jiha ta tabka shi yasa ba a gayyace su ba wajan taro.
Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Katsina Hon. Salisu Majigiri ya bayyana haka jim kadan bayan da hukumar ta sanar da ranar 11 Ga watan Aprilu 2022 a matsayin ranar da za a gudanar da Zaban Kananan Hukumomi a jihar Katsina.
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Katsina, Ibrahim Bako Malumfashi ya bayyana ranar Zaban tare da fadin cewa sun kammala duk wasu shirye-shirye domin gudanar da Zaban.
Haka shugaban jam’iyyar adawa ya kara da cewa hukumar zaban ta yi dingushe da tasgaru wajan bayyana tsare-tsaran nata, yana cewa ba a fadi yadda Zaban zai gudana ba.
“ita wannan hukumar zaban bata bayyana yadda za a yi wannan zaban ba, shin za a yi shi ta hanyar zamani ko kuwa ta hanyar da aka saba gudanar da zabe, duk ba a wannan bayyanin ba” inji shi
Haka kuma Hon. Salisu Majigiri ya koka da yadda hukumar zaban bata fitar da tsare-tsara da jadawalin zaban ba, wanda shi ne zai ba sauran jam’iyyu dama suma su tsara na su jadawalin domin tunkarar zaban kamar yadda aka tsara.
“idan babu jadawalin zaban, ta ya ya jam’iyya zata tsara yadda zata fara sayar da form da tantance ‘yan takarar da yin zaben fidda gwani da kuma yakin naman zabe, wannan ya nuna rashin shiri da kin bin ka’ida wanda kila ita ce ta haifar da kin gayyatarmu, domin ba mu ga takardar gayyata ba” inji Majigiri
Kamar yadda kungiyar gammayar jam’iyyun siyasa ta IPAC ta bayyana cewa an gayyaci kowace jam’iyya, sai dai Majigiri ya ce ba su ga takardar gayyata ba akan wannan taro.
A kwanakin baya an rawaito shugaban jam’iyyar PDP na jihar Katsina Hon. Salisu Majigiri yana bayyanin cewa sun shirya tsaf domin tunkarar wannan zabe na kananan hukumomi da za a yi, sai kuma gashi an fara saka da bakin zare ba su halarci taron farko da aka gudanar ba.
