September 18, 2026

Ku Karawa Ba ‘Yan Wasan Katsina United Kwarin Gwiwa Domin Samun Nasara – Mai Horas da ‘Yan Wasan

0

Anyi kira ga magoya bayan kungiyar wasan kwalo kafa ta Katsina United da su kara ba su goyan baya domin samun kwarin gwiwar cigaba da taka leda tare da samun nasara a wassaninsu da ke gaba.

Wannan kiran yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na wannan kungiya Nasir Sani Gide ya sanyawa hannu sannan ya rabawa manema labarai a Katsina ciki har da kafar Popular News Hausa.

Nasir Sani ya ce kiran ya fito ne daga mai horas da ‘yan wasan Azeez Muhd Audu wanda ya yi kira ga magoya bayan Kungiyar da su kasance masu hakuri tare da kara ma ‘Yan wasan kwarin gwiwa domin Kungiyar ta cigaba da samun nasara

“Coach Azeez Muhd Audu Yayi wannan Kiran ne Jim kadan bayan Kungiyar ta Katsina United ta doke takwarar ta Gombe United da ci biyu da daya, a wannan satin da ya gabata” inji sanarwar

Mai horas da ‘Yan wasan ya nemi karin goyon baya ga masu kishin Kungiyar tare da baiwa ‘Yan wasan uziri sakamakon da dama daga cikin su baki ne, wanda yace yanzu suke fahimtar junan su.

Daga karshe ya bada tabbacin shi ga dumbin magoya bayan Kungiyar wajen cigaba da fiddo sabbin dabaru da zasu sa kungiyar ta samu gagarumar nasara a kakar wasan ta bana.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *