Hukumar Gudanarwar Katsina United Ta Kafa Kwamitin Da Zai Tantance Yan Wasan Da Aka Gayyato.
Hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafar Katsina United ta kafa kwamiti mai mutane 7 da zai gudanar da tantance yan wasan da aka gayyato da ke taka leda a cikin gida.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in watsa labaran hukumar gudanarwar kungiyar Nasir Gide ya sanya ma hannu.
Kamar yadda sanarwar ta bayyana, an dora ma kwamitin alhakin zabo yan wasan da ke taka leda masu hazaka.
Sanarwar ta bayyana, an kafa kwamitin ne mai mutane 7 domin tabbatar da gaskiya a cikin aikin tantancewar.
Membobin kwamitin sun haɗa da Hussaini Garba Rossi, Alhaji Idris Ibrahim Babanta, Alhaji Sirajo Umar Baba Malumfashi, Alhaji Aminu Jariri, Aminu Musa Funtua, Koch Yahaya Lawal, sai kuma Haladu Sadauki a matsayin sakataren kwamitin.
Ana dai tsammanin membobin kwamitin za su kasance a filin wasa na Muhammad Dikko da ke cikin birnin Katsina ranar Laraba 28 ga watan Satumbar shekarar 2022.
