Dan Takarar Da Jam’iyya Ta Tsaida Kadai Zamu Aminta Da Shi – Hukumar Zabe Ta Katsina
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Katsina ta bayyana cewa Dan takarar da jam’iyyar siyasa kawai ta tsaida za su amince da shi a matsayin dan takara.
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na jihar Katsina, Alhaji Bako Malumfashi ya bayyana haka lokacin da yake fadin ranar da hukumar zata gudanar da zaban Kananan Hukumomi a jihar Katsina.
Ibrahim Bako Malumfashi ya ce a gwamnatance sun fitar da ranar 11 Ga watan Aprilu 2022 a matsayin ranar da za a gudanar da zabe fadin jihar Katsina baki daya.
Haka kuma ya shawarci masu ruwa da tsaki musamman jam’iyyun siyasa da su yi amfani da tsare-tsare da dokokin zaban Kananan Hukumomi na jihar Katsina wanda ya ce tsare-tsara da kuma jadawalin zaban za a raba su kowane lokaci ga jam’iyyun siyasa.
“Da yau 11 ga watan janairu 2022 zuwa 11 ga watan Aprilu 2022 wanda ya bada kwanakin casa’in daidai su ne wanda dokar zabe ta 2010 ta bada, a hukumance da za a yi amfani da su wajan gudanar da saba ” inji shi.
Ya kara da cewa duk wasu shirye-shirye na yakin naman zabe za su fara ne daga ranar 11 ga watan janairu 2022 har zuwa awa 24 kafin ranar zabe, sannan ya ce za a gudanar duk wasu al’amura na siyasa cikin kwanciyar hankali da lumana ba tare da hayaniya ba.
Alhaji Ibrahim Bako Malumfashi ya kara da cewa za su cigaba da gayyatar masu ruwa da tsaki akan sha’anin siyasa domin tattauna mahimman batutwa da suka shafin wannan zaban.
