September 18, 2026

Bala Abu Ga Jam’iyyar PDP: Baku Da Hadin Kan Da Zaku Iya Shiga Zabe A jihar Katsina

0

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Mataimakin shugaban jam’iyyar APC Na jihar Katsina, Alhaji Bala Abu Musawa (Cigarin Musawa) ya bayyana cewa duk arewa maso yamma babu inda jam’iyyarsu ta APC take zaune lafiya kamar jihar Katsina.

A cewarsa hakan ya biyo bayan adalici da kyakkywan jagorancin gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari wanda kullin abinda yake son ganin shi ne kan ‘ya ‘yan jam’iyyar ya hadu wurin guda domin samun nasara baki daya.

Bala Abu Musawa yana wannan bayani ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Katsina jim kadan bayan da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Katsina ya bayyana ranar da za a gudnar da zaban kananan hukumomi a jihar da ta kwashe shekaru shida babu shugabancin a kananan hukumomin

Alhaji Bala Abu Musawa (cigarin musawa) ya cigaba da cewa shi dai ban ganin akwai jam’iyyar PDP a jihar katsina, saboda har yanzu ba su shirya yin adawa ba, saboda na farko kansu ba haɗe yake ba, wa zai yi masu fastocin da kama masu ofisoshin yaƙin zaɓen saboda rarrabuwar kawunan dake tsakanin su, ina shakkun shigar zaɓen na su saboda matsalolin da suka dabaibaye su a halin yanzu.

Mataimakin shugaban jam’iyyar ya kara da cewa tun bayan da aka rantsar da su a shekarar da ta gabata, gwamna Masari ya ce aikin da da su fara shine zaɓen kananan hukumomi, ya kuma kafa kwamiti karkashin shugaban ma’aikatansa, Alhaji Muntari Lawal domin tantace wa da tsara yadda za’a gudanar da shi.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *