PDP ta tsayar da Sanata Yakubu Lado Ɗan Takarar Gwamnan Jihar Katsina
Jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Katsina ta tsayar da sanata Yakubu Lado Ɗanmarke a matsayin wanda zai yi mata takara a zaɓen 2027.
A lokacin da yake sanar da sakamakon zaɓen fidda gwani da ya gudana a shalkwatar jam’iyya da ke Katsina, jami’in zaɓen Nura Ƙanƙara ya bayyana cewa an gudanar da zaɓen ne bisa tanadin doka.
Ya ƙara da cewa, kimanin mutane 77,085 aka tantance su domin kaɗa kuri’ar amincewa da Sanata Yakubu Lado a matsayin wanda zai takara ƙarkashin jam’iyyar PDP a Katsina
Jim kaɗan bayan kammala zaɓen fidda gwanin an bayana sakamakon zaɓen inda ya nuna wakilai 77,013 ne suka kaɗa kuri’ar amincewa da Sanata Yakubu a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar Katsina a ƙarƙashin jam’iyar PDP
Da yake jawabi shugaban jam’iyyar PDP na jihar Katsina Malam Nura Amadi Kurfi ya ce jam’iyyar PDP ta amince da Sanata Yakubu a matsayin ɗan takara ɗaya tilo da zai yi mata takara a zaɓen 2027
Malam Nura Amadi Kurfi ya bayyana ɗan takarar ta su a matsayin mutum goggagen ɗan siyasa wanda yake da kwarewa da sanin makamar aiki, wanda suke da tabbacin zai sake fasilin sabuwa jihar Katsina idan ya samu nasara.
Shima a nasa jawabin ɗan takarar gwamnan jihar Katsina Ƙarƙashin jam’iyar PDP Sanata Yakubu Lado ya nuna godiyar sa ga ‘ya ‘yan jam’iyyar bisa amincewa da suka yi da shi a matsayin ɗan takara.
Ya yi alƙawarin tabbatar da wannan amana ta hanyar samar da shugabanci na kowa da kowa, gaskiya da kuma manufofin da za su amfani al’umma idan aka zaɓe shi a matsayin gwamna.
