Al’ummar Katsina sun gamsu da gwamnatina da kuma ta shugaba Tinubu. -Dikko Raɗɗa
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana cewa al’ummar jihar Katsina sun gamsu da ayyukan gwamnatin sa ƙarƙashin manufar gina gobanka.
Sannan ya ƙara da ce mutanen jihar ta Katsina sun gansu da kyakkyawan manufofin shugaban ƙasa Bola Tinubu na ‘Renewed Hope’
Gwamnan ya yi wannan maganar ne a jim kaɗan bayan kammala taron fidda gwani wanda ya tabbatar da sanarar sa ta sake samun tikitin tsayawa takarar gwamna a karo na biyu.
Haka ya bayyana cewa fitowar jama’a alama ce ta nuna gamsuwa da jam’iyyar APC tare da fatan zata yi nasara a zaɓe mai zuwa.
Ya ƙara da cewa an gudanar da zaɓen fidda gwani cikin gaskiya da tsari da lumana tera da baiwa kowa damar amfani da hakkin sa na yin zaɓe ba tare da wata matsala ba
“Zuwa yanzu jama’a sun fara ganin sauye-sauye da gwamnatin jihar Katsina ke kawowa a fannoni daban-daban abinda ke sawa suna samun ƙwarin gwiwar marawa jam’iyyar APC baya.” Inji shi
Kazalika gwamna Raɗɗa ya yabawa ‘yan takarar majalisar tarayya da dokokin da suka samu nasarar samun tikiti, yana mai bayyana ƙwarin gwiwar cewa za su wakilci al’umma kamar yadda ya kamata.
Ya kuma jinjinawa tsofaffin gwamnoni Ibrahim Shehu Shema da Aminu Bello Masari, da sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar bisa gudummawar da suka bayar wajen tabbatar da nasarar gudanar da zaben.
Bugu da ƙari, gwamnan ya yaba wa shugaban kwamitin tabbatar da ’yan takara na APC, Dakta Yakubu Ahmed Maccido, bisa yadda ya gudanar da aikin cikin gaskiya da adalci.
A ƙarshe, Gwamna Raɗɗa ya nuna cikakken yaƙinin cewa APC za ta yi nasara a babban zaɓen shekarar 2027, tare da sake tabbatar da shugaba Bola Ahmed Tinubu a kan mulki karo na biyu.
Ya buƙaci dukkan mambobin jam’iyyar da magoya baya da su ci gaba da haɗin kai tare da ƙara ƙaimi wajen shirye-shiryen yakin neman zaɓe domin tabbatar da nasara a dukkan matakai.
