Har Yanzu Ana Kan Aikin Ceto Zamfara, In Ji Gwamna Lawal Yayin Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓe
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta ci gaba da aikin ceto jihar, yana mai cewa har yanzu ba a kammala wannan manufa ba, kuma ana ci gaba da ƙoƙarin ganin an cimma ta.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata, lokacin da ya ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamnan Jihar Zamfara na jam’iyyar APC, a cibiyar taro ta Dome Arena da ke Gidan Gwamnatin Jihar a Gusau.
A ranar Lahadin da ta gabata ne reshen jam’iyyar APC na jihar Zamfara ya sanar da sunayen mambobin kwamitin, wanda aka ɗora wa alhakin tsarawa da jagorantar harkokin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar gabanin babban zaɓen shekarar 2027.
A yayin bikin ƙaddamar da kwamitin, an miƙa takardun naɗin muƙami ga babban daraktan yaƙin neman zaɓen, Alhaji Mai Buhu Gummi, da sauran mambobin kwamitin.
Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Lawal ya bayyana ƙaddamar da kwamitin a matsayin wani muhimmin mataki na ƙarfafa jam’iyyar, inganta kyakkyawan shugabanci da kuma tabbatar da kyakkyawar makoma ga al’ummar Jihar Zamfara.
Ya ce, “Lokacin da muka karɓi ragamar mulki a shekarar 2023, mun ɗauki alƙawarin ceto Zamfara, sake gina hukumominta da kuma dawo da martabar shugabanci. Yanzu kusan shekaru huɗu kenan da fara wannan tafiya, kuma mun tabbatar ta hanyar manufofi masu ma’ana, sauye-sauye masu ƙarfi da kuma zuba jari a muhimman fannoni cewa Zamfara za ta iya farfaɗowa.
“Gwamnatimmu ta samu gagarumin ci gaba a fannonin ilimi, kiwon lafiya, samar da ababen more rayuwa, gyaran harkokin aikin gwamnati da bunƙasa tattalin arziki.
“Haka kuma, ba mu yi ƙasa a gwiwa ba wajen tunkarar matsalolin tsaro da suka addabi al’ummominmu.”
Gwamnan ya kuma jaddada cewa, dole ne a ba da muhimmiyar kulawa ga ƙoƙarin sake zaɓen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR, da kuma dukkan ’yan takarar jam’iyyar da ke neman muƙaman zaɓe, a cikin tsare-tsare da shirye-shiryen siyasar APC.
A cewarsa, yayin da ake shirin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027, ya zama wajibi yaƙin neman zaɓen jam’iyyar ya dogara da ayyukan da aka aiwatar, ya samu karɓuwa ta hanyar amana, ya ƙara ƙarfi ta hanyar haɗin kai, sannan a bar al’umma su ne za su tantance nasararsa.
Ya ce, “Kada mu ɗauka cewa za mu samu nasarar zaɓe kai tsaye saboda kawai muna kan mulki.
“Ikon siyasa amana ce mai girma da aka ɗora wa shugabanni, don haka dole ne a ci gaba da neman amincewar masu zaɓe. Ayyukan da muka gudanar su ne za su yi mana magana, amma kuma wajibi ne mu riƙa yi wa al’ummarmu magana cikin gaskiya game da ƙalubalen da har yanzu suke gabanmu da kuma damarmakin da ke tafe.
“Dole ne mu kai saƙonmu zuwa kowace gunduma, rumfar zaɓe, ƙauye da al’umma a faɗin ƙananan hukumomi 14 na Jihar Zamfara.
“Dole ne mu saurari al’ummarmu, mu fahimci abubuwan da ke damunsu, bayyana musu manufofinmu tare da nuna dalilin da ya sa ci gaba da ingantaccen shugabanci yake da muhimmanci wajen karewa da bunƙasa nasarorin da aka riga aka samu.”
