‘Yan bindiga sun harbe jarumar fim har lahira
DAGA IRO MAMMAN
WASU ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun harbe wata jarumar
finafinan Nollywood mai suna Ngozi Chiemeke a jiya.
Rahotanni sun ce abin ya faru ne a titin Deeper Life a garin Boji-Boji Owa da ke Ƙaramar Hukumar Ika North-east ta Jihar Delta.
Mujallar Fim ta gano cewa an kashe jarumar mai tasowa ne a shagon ta na sana’ar hadahadar kuɗi na P.O.S.
Mutanen unguwar sun ce su dai sun ji tashin bindiga a wajajen shagon, to amma kafin su kai ɗauki har maharan sun arce daga wurin.
Ba a san dalilin kisan ba. Ngozi Chiemeke a lokeshin ɗin ɗaukar wani fim
An ɗauki gawar Ngozi Chiemeke an kai ta mutuware an aje kafin a yi mata jana’iza.
Kisan gillar ya haifar da babban ruɗani da baƙin ciki a garin, inda mutane su ka riƙa taruwa gungu-gungu su na tattaunawa a kai. Jami’in yaɗa labarai na rundunar ‘yan sanda ta jihar, DSP Bright Edafe, ya tabbatar da labarin kisan ga ‘yan jarida, ya ce, “Wasu maza da ba a san ko su wanene ba su ne su ka kashe matashiyar matar, amma an fara ƙoƙarin kama waɗanda su ka aikata wannan abu
