GWARAZAN SHEKARA TA 2021: Sanata Ahmad Babba Kaita Da Hon Ali Mansur Mashi.
Daga Abubakar Karare
Sanata Babba Kaita
Sanata Babba Kaita shine wanda kusan aka sallama cewa ya yi zarra, ya zama gwarzon shekara don ya yi ma sauran takwarorinsa nisa, domi an tabbatar kananan hukumomi 12 da yake wakilta a zauren majalisa ta kasa da bata samun aikin daga wakilcinsa ba.
Idan aka duba duk wata karamar hukuma da ke yankin Daura inda yake wakilta babu wata karamar hukuma da ke da ƙasa da ward goma, kuma akalla cikin ward sama da 120 waɗanda ke ƙarƙashinsa babu ward din da babu ayyukan Sanata Ahmad Baba Kaita.
Sannan akalla ya gina asibitoci na mata masu haihuwa guda goma sha takwas 18 tare da kayan aiki, ya gina ƙarin azuzuwa a makarantun mu na boko wanda shi kanshi bai san iya yawansu ba, sannan ya gina rijiyoyi masu aiki da hasken rana.
Sauran ayyukan da ya kawo suna hada da gina islamiyoyi ya bada transfomomi, ya gina tsanya ta ruwa, yayi Gadoji sannan ya samama mutane ayyuka a matakin gwamnatin tarayya, wannan wasu daga cikin ayyukan Sanata Ahmad Baba Kai mai wakiltar shiyyar Daura a jihar Katsina .
Hon Mansur Ali Mashi.
Ɗan majalisa mai wakiltar Mashi da Dutsi a majalisar tarayya, ya zama gwarzon shekara ne saboda babu wani Ɗan majalisa da ya kai shi tallafama matasa da kayan sana’a, ya raba ‘Ƴar ƙurƙura, (NAPPED) keken ɗinki, injin ban ruwa, mashina, tare da motoci kusan ya dauki dogon lokaci duk sati sai kaji yayi empowerment watau bada tallafi.
Mafi karancin tallafin shi na kuɗi shine dubu ashirin 20k ga masu ƙananan sana’oi, sannan ya gina asibitoci na mata masu haihuwa kuma ya gina ƙananan asibitoci (Dispensery) bangaren ilimi kuma ya gina ƙarin azuzuwa a makarantu, ya gina Dam domin amfanar mutane da dabbobi ga kuma inganta noman rani ga manoma uwa uba kuma ya samarma ɗumbin mutane aiki a gwamnatin jiha da ta taraiyya.
Haka kuma Hon Mansur Ali Mashi mataimakin chairman ne na committee a zauren majalisa amma da yake zuciyarshi tsaye take ya yi abinda masu rike da shugabancin committee ba suyi ba.
A cikin dogon nazarin da na yi Wadannan sune suka yi zarra wurin talakawan jihar Katsina saboda su sun hada abubuwa da yawa wanda suka shafi masu ilimi, Talakawa manoma ‘yan siyasa da mutanen karkara kowa ya amfana da wakilcinsu.
