Yau Alhamis Za a fara Gudanar Da Taron Bikin KILAF Award 2025 A Kano
DAGA MUKHTAR YAKUBU
A yau Alhamis 6 ga nuwamba 2026 ne za a shiga rana ta farko ta taron bikin bajekolin finafinai na Afirka da kalankuwa da aka saba yi a Kano duk shekara,mai taken “Kano Indigenous Languages Afrka Film Market and Festival”.
Taron wanda za a gudanar da shi na tsawon kwanaki 3 , wato daga ranar alhamis 6 ga Nuwamba zuwa asabar 8 ga nuwamba, in da za a gudanar da muhimman abubuwan da suka hada da lakcoci da kalankuwa, bajekolin kayayyakin gargajiya na Afirka da suka hada da abinci riguna da Zane zane da sassake sassake na Afirka, da kuma bikin bayar da kyautuka ga finafinan da suka yi nasara a gasar da suka shiga ta wannan shekarar.
Kamar dai yadda takardar Jadawalin taron da kwamitin tsara taron ya fitar ta nuna, za a fara taron ne tun da misalin karfe 9 na safe a Sabuwar Jami’ar Bayero, inda za a fara da maraba da baki da kuma tantance finafinan da suka shiga Gasar.
Sai kuma gabatar da abincin gargajiya na Afirka Wanda aka saka masa suna “African Kitchen” Duk a DBS dake cikin sabuwar Jami’ar Bayero. Tun daga karfe 9 na safe har zuwa karfe 9 na dare.
A rana ta biyu kuwa waro Juma’a 7 ga Nuwamba za fara ne da yawon bude idanu, da misalin karfe 9 na safe, inda za a zagaya da baki mahalarta taron cikin garin Kano domin nuna musu tsarin al’adun garin Kano da masarauta da sauran abubuwan tarihi da al’adu,.
Haka nan a kwai cin abinci na musamman da kungiyar Dattawan Arewa ACF ta shirya wahalarta taron da sauran abubuwada dama da za a gudanar.
A rana ta karshe na taron akwai bita a kan fim da kuma Jawabi a kan Mata da aikin Jarida.
Haka nan a ranar ce za bayyana sunayen Jarumai da kuma finafinan da suka yi nasara a gasar wato “Award Night” a dakin taro na Otal din Bristol.
Tuni dai manyan baki suka fara halarta daga sassa daban daban na duniya da suka hada da Afirka Turai da kuma yankin Asiya.
