September 17, 2026

Furodusa Isah Doro Ya Fito Da Sabon KUDIRI

FB_IMG_1757947649245

DAGA MUKHTAR YAKUBU

Matashin furodusa Isah Bawa Doro, wanda a yanzu Tauraruwar sa take haskawa ya ƙara yin wani yunkuri na samar da gawurtaccen Fim mai suna Kudiri, wanda a yanzu haka aka fara haska tallan sa channel din sa na Youtube a tashar Kannywood Exclusive TV, domin ya kasance taba ka lashe kafin gundarin shirin ya fara zuwa.

Fim ɗin Kudiri ba wai Fim ba ne kawai. Labari ne Mai ɗauke da rikici, kauna da ɓoyayyun sirrika da za su girgiza zukatan masu kallo.

Za dai a fara gundarin shirin na Kudiri ne a ranar Alhamis 18 ga Satumba 2025 da misalin karfe 8 na daren kowacce Alhamis a dai channel ɗin sa na Kannywood Exclusive TV.

Isah Bawa Doro, shi ne furodusan fim ɗin, ya yin da ƙwararran Darakta Hafizu Ballo ya kasance mai bada Umarni.

About The Author