September 17, 2026

Furodusa Sani Sule Katsina Zai Aurar Da ‘Yarsa Ramlat

IMG-20251106-WA0029

 

DAGA MUKHTAR YAKUBU

Shugaban Kamfanin shirya finafinai na Rite Time Maltimidia Ltd Alhaji Sani Sule Katsina,(Garkuwa) zai bikin auren ‘yarsa Ramlat Sani Sule inda za a aurar da ita ga Ismail Shehu Shehu (Santali)

Za a daura auren ne dai a ranar Juma’a 7 ga Nuwamba da misalin karfe 2 na rana a Masallacin Juma’a na Murtala da Unguwar Hausawa a cikin garin Kano.

A wani saƙo na gayyata da Alhaji Sani Sule Katsina ya aikawa wakilin mu ya sanar da gayyatar dukkan abokan sana’ar sa ‘yan fim da sauran Masoya da bakan arziki zuwa wajen taron shaidar daurin auren. Kuma wadanda ba su samu damar harlarta ba su taya da addu’ar Allah ya baiwa ango da amarya zaman lafiya da karuwar arziki.

About The Author