September 18, 2026

Wasu Gwamnonin Najeriya Na Amfani Da sunan Shugaba Buhari a Matsayin Uzurin Nuna Gazawar su. -Femi Adesina

0

Mai ba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin yada labarai Femi Adesina, ya zargi wasu gwamnonin jihohin kasar da yin amfani da sunan Shugaba Buhari sa a matsayin uzurin nuna gazawar su.

Majiyar DCLHausa ta gidan talabijin na Channels ta ce, Adesina ya wallafa hakan a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, inda ya yi zargin cewa irin wadannan gwamnonin na neman matsayi na jarumta ne ta hanyar cin zarafi ga shugaban kasa.

“Idan suna bin albashi da fansho, da zarar watan ya kare, sai su fara cin mutuncin Shugaban kasa, suna tunanin jama’arsu za su manta da albashin da ba a biya ba da kuma fansho,” inji shi.

DCL Hausa

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *