Wasu mahara sun kashe shugaban hukumar KADGIS.
Daga Auwal Isah
An kashe Malam Dauda ne yau Juma’a a gidanshi dake unguwar Barakallahu cikin karamar hukumar Igabin jihar Kaduna.
Jaridar Leadership ta bada rohotan cewa, maharan sun kutsa kai gidan ne ta wata barauniyar hanya inda suka kashe shi, ba tare da daukar komai a gidan ba.
Kuma maharan bayan kashe babban jami’in gwamnatin, sun kai hari ga wata al’umma a lokacin da suke barin wurin, amma dai ba a samu rohotan jikkatar kowa ba.
Da yake tabbatar da lamarin ga manema labarai, hakimin yankin Alhaji Muhammad Abdullahi ya bayyana cewa DPO mai kula da ofisosin yan sanda na Rigachikun da Barnawa ya je wurin da lamarin ya faru.
Kuma kamar yadda ya bayyana, dama mutumen suka zo kashewa, saboda gidanshi sukai ma tsinke kai tsaye, suka kashe shi, tare da yin tafiyarsu basu dauki komai ba, ko kuma taba wani a gidan.
