Zamfarawa sun yi ƙorafi kan yadda Gwamna Matawalle ke tsallen-gada bisa rahoton kwamitin da ya bankaɗo masu laifi a kashe-kashen jihar.
Gwamna Matawalle ya bai wa Majalisar Dokoki da Kotunan Zamfara ‘yancin gashin kan su
Al’ummar Jihar Zamfara na ci gaba da nuna damuwar su kan yadda Gwamna Bello Matawalle ya ƙi yin amfani da shawarwarin Da Rahoton Kwamitin Musabbabin Rikicin Zamfara Da Yadda Za A Magance Shi a jihar.
Kwamitin dai a cikin 2019 ne Gwamna Matawalle ya kafa shi da kan sa, wanda aka ɗora tsohon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Mohammed Abubakar a matsayin Shugaban Kwamiti.
Kwamitin ya miƙa wa gwannan rahoton abin da ya bankaɗo, kuma ya lissafa waɗanda ke da hannu, yawan asarar da aka yi, waɗanda aka kashe da waɗanda aka raba da gidajen su.
Hatta yawan marayu da zawarawa mata da masu takabar da aka mutu aka bari, duk kwamitin ya lissafa.
Kuma ya lissafa waɗanda za a hukunta, saboda samun su da haɗa baki da ‘yan bindiga. Tun cikin Oktoba 2019 kwamitin ya miƙa wa gwannan rahoton sa.
Yayin da Gwamna ke cewa ya yi aiki da wasu shawarwari da kwamitin ya bayar, al’ummar Zamfara na cikin halin nuna rashin yarda da hakan. Su na zargin gwamnan ya na tuma tsallen gada kan rahoton, ya na tattake shi.
PREMIUM TIMES a cikin 2019 ta buga labarin kwamitin ya ce ya yi nazarin lamarin ‘yan bindiga a Jihar Zamfara, tun daga Yuni 2011 zuwa Mayu 29 na shekarar 2019, ranar da Matawalle ya kama mulki.
Daga 2011 zuwa 2019 ɗin kuwa, duk lokacin tsohon Gwamna Abdul’aziz Yaro ne da Matawalle ya gada.
Matawalle ya kafa kwamitin a lokacin da ya ke cikin jam’iyyar PDP. Sai dai kuma a yanzu ya na cikin jam’iyya mai mulki, wato APC.
A lokacin da aka damƙa masa rahoton, Abubakar Shugaban Kwamiti ya ce tsakanin 2011 zuwa Mayu 2019 matan aure 4,983 sun rasa mazajen su, waɗanda ‘yan bindiga suka kashe.
Kwamitin ya ce a wadancan shekaru an samu yaran da aka maida marayu su 25,050. Sannan kuma an raba mutum 190,340 daga gidajen su.
Rahoto ya ci gaba da nuna cewa Fulanin da ba su ji ba, ba su gani ba sun rasa shanu 2,015, tumaki 141, jakai da raƙuma 2,600 sai kuma an yi asarar motoci da babura da sauran ƙananan ababen hawa 147,800 waɗanda aka banka wa wuta a yankuna daban-daban na ji
