September 17, 2026

Wanene Sanata Sa’idu Muhammad Ɗan Sadau?

0

Wasu Muhimman Batutuwa Da Ya Kamata A Sani Game Da Shi

SANATA SAIDU MUHAMMAD DANSADAU shine shugaban kwamitin masallacin rukunin gidajen ‘yan majalisu da ke Apo a cikin babban birnin Tarayya Abuja .

Jiya Asabar kwamitin masallacin na APO ya bayar da sanarwar dakatar da babban limamin masallacin DR. Nura Khalid daga limancin masallacin, bisa abinda kwamitin masallacin ya Kira da yunkurin tunzura jama’a su yi wa gwamnati bore .

Kwamitin masallacin ya ce kamata yayi sheik Nura Khalid ya ce wa al’umma su ki zabar wadanda suka kasa wajen tsare rayukansu, maimakon yace kada jama’a su yi zabe kwata-kwata.

  1. An haifi Sanatan a ranar 20 ga watan Yuni na shekara ta 1953, kenan yanzu shekarunsa na haihuwa 69.
  2. Ya wakilci shiyyar Zamfara ta tsakiya a Zauren majalisar Dattawa ta Tarayya daga 1999 zuwa 2003 a karkashin tutar jamiyyar APP,
  3. An sake zabarsa a Karo na biyu a shekara ta 2003 zuwa 2007 a karkashin tutar jamiyyar ANPP
  4. Shine Sanatan da ya fara tayarda kura a kan lallai sai Senate President na wancan lokaci Sanata Adolphus Wabara ya sauka daga kujerarsa bisa tuhumar karbar wasu makudan dalolin Amurka da ake zargin yayi a matsayin cinhanci, kuma daga karshe dai dole shugaban Sanatocin sai da ya sauka.
  5. Yana daya daga cikin Sanatocin da suka fi yin fice wajen yakar tazarcen tsohon shugaban kasa Olisegun Obasanjo, daga 2006 zuwa 2007, tare da marigayi Sanata Sule Yari Gandi
  6. Ya nemi tsayawa takarar Gwamnan jihar Zamfara a kakar zabe ta 2007, Amma bai samu nasarar samun tikitin jamiyyarsa ta ANPP ba . Daga bisani a shekara ta 2008 ya fice daga jamiyyar sa ta ANPP, tare da ayyana ficewarsa daga harkokin siyasa baki daya, inda ya tsunduma kai’n da nai’n cikin shaanin aikin gona.
  7. Ya sake dawowa cikin harkokin siyasa inda a shekarar 2019 ya kaddamar da jamiyyar ceton Nigeria ( Nigerian Rescue Mission NRM ) mai taken ” talauci bai hana takara ” ( not too poor to tun )
  8. Jiharsa ta Zamfara ita ce tushen inda aka faro matsalar Fulani yanfashin daji.masu kashe mutane da garkuwa don neman kudin fansa
  9. Karamar Hukumarsa ta Maru ita ce inda matsalar ta fara bayyana a cikin shekarun 2010 zuwa 2011 .
  10. Yankin da ya fito na Dansadau da Dangulbi, da Dankurmi a can ne aka fara ganin kisan bai daya mafi muni da fulani barayin daji suka fara yi, inda a rana daya aka kashe sama da mutane 160 cikin shekarar 2011.
  11. Shine fitaccen Dan Arewa mafi daga murya da fafutukar ganin an kawo karshen matsalar tsaro a jiharsa ta Zamfara da Arewa baki daya .
  12. Shine ya jagoranci kafa kungiyar dattawan jihar Zamfara ( Zamfara Elders Forum ) kungiyar da tafi kowace matsin lamba ga gwamnati a kan tabarbarewar tsaro a Arewa .
  13. Sanata Saidu Muhammad DANSADAU baya tare da gwamnatin Buhari, hasali ma yana daya daga cikin na gaba gaba wajen sukar gwamnatin Buhari, musamman a kan batutuwan da suka shafi yaki da rashawa da tabarbarewar tsaro .

Abinda kawai ya bambanta su da sheik Nura Khalid shine cewa da shehin yayi kada mutane su yi zabe kwata-kwata, shi a ganinsa mutane su sauya shugabannin da basu gamsu da su ba, shine daidai ba wai su ki yin zabe ba.

Saboda haka, ya kai dan’uwa, ko yar’uwa kamin ku zagi, ko ku muzanta Sanata Said Muhammad Dansadau, ku fara bincike tukun ku gano ko kun fishi bayarda gudummuwa wajen neman mafita daga matsalar tsaro ko kuwa .

A matsayinka na mai hankali ka auna da iliminka da tunaninka ta Ina kin yin zabe kwata-kwata zai samarwa da al’umma mafita ? In dai so kake ka tursasa wa gwamnati ko masu mulkin siyasa su yi abinda kake so, to barazanar zaben wani ba su ba, yafi tasiri fiye da barazanar kin yin zabe kwata-kwata.

Don haka a wannan matsalar Sanata Said Muhammad Dansadau yafi gaskiya , sai dai ban sani ba ko dakatarwar ita ce mafi aala ko kuma akwai wata hanyar warware matsalar daban. Allah shine mafi sani.

Yazid Nasudan
03)04/2022

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *