2023: Ina Da Sabon Tunani Game Da Matasan Katsina Ta Tsakiya – Hon. Sani Aliyu Ɗanlami
Kwamishinan ma’aikatar harkokin Jindadi da Wassani Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya bayyana wasu shirye-shirye da yake da su akan matasan Katsina ta tsakiya sakamakon halin Ni ‘ya su da suka da rashin shuagabancin a matakin tarayya
Hon. Sani Aliyu ya ce ya zame masa wajibi ya amsa kiraye-kirayen da jama’a ke yi masa domin tunkarar matsalar da matasa suka shiga saboda rashin jagoranci a matakin tarayya.
Ya zuwa yanzu dai babu wani ɗan siyasa a jihar Katsina da ke fuskantar kiraye-kirayen jama’a na ya dawo domin neman kujerar majalisar tarayya a Katsina ta tsakiya, ga alama yana daga da amsa wannan kiran.
Haka kuma alamu na nuni da cewa su kan su matasan Katsina suna kan gaba wajan ganin Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya dawo kan kujerar sa domin ya dawo da martabar matasan Katsina ta tsakiya
Kasancewar Sani Aliyu mutum na matasa ya sanya dole yanzu ya yi wani abu dai zai taimakawa matasa wajan ganin sun dawo cikin hayyacisu duba da irin yadda aka mai da su baya ta kowane ɓangare.
Hon. Sani Aliyu Ɗanlami ya jaddada bukatar da ke akwai na ganin an fitar da kitse da wuta domin su ma matasa sun da hakkin da ya kamata a lura da shi kuma yi wani abu akai domin shiga cikin lamarin su.
“A matsayina na kwamshiinan Jindadi da walwala da Wassani zan yi duk mai yiyuwa wajan ganin na tallafi matasan Katsina ta tsakiya saboda an bar su ba aikin yi, ba tallafi ba taimako” inji shi.
Lokacin da Hon. Sani Aliyu Ɗanlami yake ɗan majalisar wakilai ta tarayyar Matasa da dama sun ci albarkacin sa ta fannoni da dama da suka haɗa da ɓangaren ilimin da da saboda da aikin gwamnati da kuma ba su jari domin dogaro da Kai.
A cewar sa duk wannan alheri da ya shinfida ya riga mu gidan gaskiya babu alamun an taimaki matasa a Katsina ta tsakiya saboda haka ya ce lallai domin ya yi sabon tunani game da su tare da kawo sabbin hanyoyin taimakon su a samu nasarar da ake buƙata.
“Babu shakka mun ɗora matasan Katsina ta tsakiya akan turba Kyakyawa amma saboda jarabawar Allah ta’ala sun shiga hali, sai dai da yake Allah ki yi mun fatan dawowa da matsayi da martabar matasan Katsina ta tsakiya insha’Allahu.” Inji Hon. Sani Aliyu
