Har Yanzu Kungiyar 13X13 Baka Yanke Hukuncin Jami’yyar Da Zata Bi Ba Tsakanin PDP Da APC A 2023
Daga El-Zaharadeen Umar Katsina
Rahotanni da muke samu yanzu sun tabbatar da cewa jagororin kungiyar 13X13 suna ƙasar Daular Larabawa (Dubai) suna tattaunawa akan wannan batun wace jami’yya kungiyar zata marawa baya a zabe mai zuwa
Wata majiya mai tushe ta tabbatarwa da kafar Popular News Hausa cewa yau kimanin kwana uku ke nan ana tattaunawa a tsakanin shuwagabannin amma ba a cimma matsaya ba.
“Muna nan Dubai suna tattaunawa akan wace jami’yya zamu goyi bayan ta a zaɓe mai zuwa tsakanin PDP da kuma APC, amma dai magana ta yi nisa so sai akan wannan batu ” inji majiyarmu.
Haka kuma Popular News Hausa ta ruwaito cewa shi kan shi jagoran kungiyar 13X13 din Dauda Kahutu Rarara yana cikin wadannan suka ziyarci Dubai domin wannan muhimmin al’amari.
A baya dai an sha bayyana cewa wannan kungiyar ta 13X13 ba ta siyasa ba ce, an kafa ta ne domin taimakon marasa karfi inda har ta fara wasu ayyuka da suka nuna haka, misalin fitar da marasa karfi daga gidan gyaran Hali, tare da ba su tallafi.
Yanzu dai an bin jira a gani, shi ne, wace jami’yya kungiyar 13X13 zata bi a kakar zaɓe mai zuwa domin cimma manufofi da kuma muradin kungiyar, lokaci alƙali.
