Tsakanin Ladin Cima Da ‘Yan Fim!
Daga: ALIYU A. GORA II
Ina mamakin yadda hirar Ladin Cima da BBC ta zama wani abin terere.
Na farko dai matar nan gani ta ke ta samu sararin amayar da abin da watakila, ya dade ya na sosa mata zuciya.
Sai dai babban abin takacin shi ne, yadda wasu marasa fahimta su ke ganin laifin wasu ‘yan fim da su ka kalubalance ta da cewa ba haka abin ya ke ba.
Ina so ku sani cewa, su BBC tun farko ya kamata su nemi jin ta bakin ‘yan fim kafin su fitar da rahoton, amma ba su yi haka ba.
Idan har ‘yan fim ba su fito sun kare kan su ba, kun ga kenan tamkar sun gaskata furucin Ladi ne.
Don haka babu laifi, idan mutum ya ce ka cuce shi, kai kuma ka ce ba ka cuce shi ba.
Sai dai lamarin ya na neman sauyawa zuwa wani nau’i na rashin adalci, inda wasu ke shaida wa duniya irin alkhairan da su ka yi mata a bayan fage, yayin da wasu ke amfani da lamarin su na furta kalaman batanci a kan ‘yan fim, wannan ba daidai ba ne.
Ga masu cewa wai a yi mata uzuri saboda tunanin yawan shekaru kuma, ni ban taba ganin fim din da aka nuno ta na furta kalaman shirme saboda tsufa ba.
Don haka babu ta inda zai zama laifi don ‘yan fim sun kare kan su, domin furucin ta zai iya bata wa Kannywood suna, kuma hakan zai iya janyo hankalin hukumomi a kan tunanin ‘yan fim su na zaluntar marasa galihu.
A ka’idar aikin jarida, babu inda aka haramta wa mutum maida martani idan an yi magana a kan sa. Don haka ina bada shawara, kada wannan ya zama hujjar da wasu za su rika amfani da ita su na tozarta ‘yan fim saboda son zuciya.
Ta ce ba a biyan ta, an ce ana biyan ta, ina hakan ya zama laifi Pls?
