September 18, 2026

Gudunmawar Biliyan Daya: Dahiru Mangal Ya Fitar Da Katsinawa Kunya.

0

Tsokaci Daga Yakubu Lawal

Bibiyar tarihi da bincike sune za su fayyace wannan batu domin lokaci ya wuce da za mu zauna daga teburin shayi don amincewa ko rashin amincewa da rubuce-rubuce koma da wace manufa aka yi su, tun da ilmi da bincike da tambaya halak ne garemu ko don gudun ranar da zamu amsa tambayoyin da bamu iya amsawa(YAUMULTIBLUL-SARA’IL).

Tunda tarihi zamu bi kadi, asali na ita kalmar ‘GIDAUNIYA’ Bahaushiyar kalma ce da Bahaushe ke nufin babban mazubi mai daukar abu mai yawa musamman fura a Kasar Hausa, anan ne aka samu ‘Gidauniyar Maigida ta Fura’

Zuwan Turawa da ya zo wa Hausawa da sabbin kayan ma’aikaci sai Bahaushe ya kalli wasu daga cikin kayan da suka yi daidai da nashi ya basu suna ciki kuwa har da Gidauniya, kuma saboda girman Gidauniya ita ce wurin zubawa Maigida abinci,don haka ko a gidan attajirai Gidauniya cikata sai an shirya.

Gidauniya kenan ta fuskar ma’ana ta zahiri.

Idan muka juya ma’anar boye,Gidauniya ga Bahaushe ta kunshi gangami da akanyi don tara wa wani dake da wata hidima kudade ko madadinsu don ya samu saukin kammala hidimar cikin sauki, da tafiya ta yi tafiya sai kalmar ta samu kishiya aka samu ‘AJO’ da akan shiryawa har ‘yan kasuwa da suka samu karayar arziki.

Irin wannan salo ya canja fasali tare da fita daga hannun Hausawa a hankali, hakan kuwa bai rasa nasaba da zumunci da ya yi rauni a tsakanin Hausawa.

Masana Fassara sun yi kokari kwarai da gaske na Fassara duk wani asusu na musamman da aka ware don wasu bukatu da sunan ‘GIDAUNIYA’ domin za ka tarar kudin cikinsa da karo-karo ake samun tarasu.

Wannan ne ya sanya ire-iren wadannan Gidauniyoyi basu lisaftuwa a matakan Kasa da Kasa da Kungiyoyi da Gwamnatocin tarayya da Jaha da Kananan Hukumomi da lakabin ‘TRUST FUND’.

Irin wannan yunkuri ne,a Jahohi irin Katsina aka samu Gidauniyar Jahar Katsina(Katsina Trust Fund),Gidauniyar Ilmin Jahar Katsina(Katsina Educational Trust Fund) da kuma Katsina Islamic Foundation wadda ita ce ta haifar da samarda Jami’ar Musulunci ta farko a Jahar Katsina wadda aka maida wa suna (Alqalam University Katsina)

Kuma duk cigaban da wadannan gidauniyoyi suka kawo a Jahar Katsina, kudin karo-karo ne daga al’ummar kasarnan harda makwabta suka cika gidauniyoyin.

Ita ma Jahar Yobe ta ga lokaci ya yi da ya kamata ta bi sahu na yin Gidauniyar Bunkasa Ilmi da ta yi wa lakabi da(Educational Development Trust Fund).

A ranar Alhamis 10 ga watan Fairairu 2022, Jahar Yoben ta Kaddamar da wannan gidauniya ta Ilmi inda hamshakin dan kasuwa, dan asalin Jahar Katsina Alhaji Dahiru Barau Mangal,ya zama mai jagoranci kuma babban mai kaddamarwa.

Da gani babu tambaya gwamnatin Jahar Yobe ta zabi wannan babban dan kasuwa ne saboda sanin cewar yana da wuyan daukar wannan aiki,domin dama duk inda aka yi yekuwar neman tallafi a kan jawo wanda gidauniyar zata kusa ciki a hannunsa ya jagoranci tara kudaden.

A wurin wannan taro shi babban mai kaddamarwa wanda shi ne shugaban rukunin kamfanin jirage na MAX-AIR da Afdin Constructions da Darma Rice Mill da sauransu Alhaji Dahiru Mangal ya bayarda irin gudumuwar da suka yi tsammani daga gareshi.

Dahiru Mangal dai ya bayarda gudummuwar kudi wuri na gugar wuri har Naira Miliyar Dubu Daya(1Billion Naira) baya ga wadanda wasu mutanen za su bayar a dalilinsa tun da dama mai zuwa ake aikawa.

Wannan bukatar ce dama ta sanya gwamnatin Jahar Yobe ta duro ruwa gora ta gayyaci dan asalin jihar Katsina ya jagoranci wannan gidauniya saboda yana da wuyan dauka.

Irin wannan tsarin ne sauran jahohi sukayi, suka cika gidauniyoyin cigaba da suke dasu, ciki kuwa har da jihar Katsina.

Wannan yunkuri na baiwa mara da kunya ya fitar da Katsinawa da Jahar Katsina kunya ga idon sauran Jahohi har da fadin Najeriya baki daya,domin ko akwai wanda ya taba irin wannan baici bai yi shuhara kamar yarda Alhaji Dahiru Mangal ya yi ba a Jahar Yobe.

Akwai dalilai da dama da za ni bayar da zasu nuna gudummuwar tsabar kudi Naira biliyan daya da Alhaji D.B.Mangal ya bayar ta fitar da Katsinawa kunya, tare mayarda bukin da aka dade ana yiwa Katsinawa.

Tarihi na nan ajiye da ya nuna mutane ne daga dukkan fadin kasarnan wanda lokaci ba zai iya barin lisaftosu ba, suka yi silar samarda ‘gidauniyar jihar Katsina da gidauniyar Ilmi wadanda har yanzu al’umma na amfana da ayyukansu sama da shekaru (20).

Ita kuwa gidauniyar musulunci da aka yi,ita ce ta haifar da Jami’ar Musulci ta farko a Kasarnan wadda ta rikide zuwa(Alqalam University),inda kaso mafi tsoka na gidauniyar har Naira Biliyan daya(1Billion) ya fito daga mai arzikin jihar Kano, Alhaji Aminu Dantata,ya yi wa Jami’ar ayyuka daban-daban da kudin.

Ta fuskar harkokin bunkasa rayuwar al’umma kuwa har daga kudancin Kasarnan an samu wani mai arziki daga yankin Neja Delta,mai (Jack Rich Foundation) ya yo tafiyayya har zuwa garin Daura ya gina wata Asibiti don al’umma.

Wadanan kadan ne daga hujjojin da zasu sanya Katsinawa su yi yabo da son barka ga hamshakin dan Kasuwar jihar Katsina,Alhaji Dahiru Barau Mangal bisa sunan arziki da ya jawo mana, tare da fatar cigaba da tallafar al’umma gida da waje.

Idan dai har babu irinsu Mangal a wasu jahohi shin mu mun samu wannan ita ce tambayar dake bukatar amsa,kafin neman dalilin bayarda gudummuwar.

Duka!Idan ba wadannan hujjoji da tarihi ya ajiye ba, zamu yi la’akari dasu sai dai muyi ta bulayin da zai samu yanke hukuncin shari’ar da babu mai kara balle wanda ake kara,don makudan kudaden da suka kai Naira Miliyan Dubu Daya sun wuce a nemi alfarma dasu sai dai don in an isa a bayarda su,inda ni da kai bamu sani ba sai dai hasashe.

Ko da Bahaushe yakance yasan dalilin harbin da Zuma ke yi,sai mu dunga kyakyawan zato,don gudun shedar zir.

Alkalamin: Y.L.Katsina
Dan Jarida
Jami’in Hulda da Jama’a
080-34331498

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *