Tsakanin Marigayi Ummaru Yar’adua Da Halinsa Wanne Aka fi So?
Tsakanin Marigayi Ummaru Yar’adua Da Halinsa Wanne Aka fi So
Daga Yakubu Lawal Katsina
Tunawa da tsohon shugaban ƙasa Marigayi Malam Ummaru Musa ‘Yar’adua (Matawallen Katsina?
Tun daga ranar 5th ga Watan Mayu na 2010 da Ajaliyar Malam Ummaru Musa ‘Yar’adua ta yi tun daga jajibirin ranar wasu al’ummar Kasar nan ba tare da la’akari da bambamcin ɓangare ko Yare, ko Akida ko Siyasa ba, a Nijeriya baki ɗaya sukan yi alhini don tunawa da Marigayi Shugaban Ƙasar Nijeriya Malam Ummaru Musa ‘Yar’adua.
Wannan kuma bai rasa nasaba da ribarsa da aka ci a lokacin rayuwarsa da kuma jagoranci abin misali
Sai dai al’ummar Jihar Katsina ita zata fi karda dalilai da dama na tunawa da wannan Shugaba da ya rigayemu gidan gaskiya Shekaru goma sha huɗu (14) kenan a wannan shekarar ta 2024
Musamman wasu Makusantansa na siyasa suke jagorantar tarukan lakcha da kuma addu’o’in samun rahamar Ubangiji a gare shi.
A wannan shekarar abin da ya ƙara ankarar da al’umma a kan Marigayi Malam Ummaru Musa Yar’adua ya cika Shekaru goma sha huɗu (14) da rasuwa shi ne taron manema labaru da wata Kungiya Mai suna Plesant Library and Book Club da ke gaba-gaba wajen ɗabbaƙa tarukan tare da kara fito da wasu batutuwa da za su iya amfanar duk mai muraɗin yin mulki a wannan duniya.

Babu shakka mutuwa wa’azi ce ga mai hankali musamman a wannan lokaci da mafi rinjayen al’umma ke da buƙatar kamanci ko madad.
An yi taron kamar yarda aka saba tare da sa albarkar Shehunnan Malamai na Addini da na Siyasa da shugabanni da Sarakuna da masu rike da Mukamai a mataki daban-daban
Gwamnan jihar Katsina Mai ci yanzu muƙarrabansa da tsohon gwamnan jihar Katsina a shekaru (8) da suka gabata dama sauran waɗanda suka maganta a bagiren sun yi tarayya a kan cewa Malam Ummaru Musa ‘Yar’adua Mutum ne mai gudun duniya da ya shinfinɗa adalci a shugancin sa da bai damu da abin duniya ba kuma koyi da shi mafita ce ga mai son ya fita
Tabbas! dukkan waɗanda suka yi wannan shaidar ga wannan shugaba da ya kaura shekaru (14) da suka shuɗe ,sun yi tarayya ce ta kut da kut da shi musamman a lokacin da ya jagoranci gwamnatin jihar Katsina daga 1999- 2007 da kuma gajeran lokacin da ya yi mulkin Nijeriya.
Ba wai a tsakanin shugabanni ba kadai, ko a bakin talakawan da Malam Ummaru Yar’adua ya mulka fatan dacewa a lahira suke yi masa duk da shekarun da ya yi zamaninsa akwai shugabancin da aka ratso bayansa da dama.
Duk da cewar a baya-bayan nan, a matakai na jiha da Ƙasa, Malam Ummaru Yar’adua shi ne shugaba da ya rigayemu, ba a samu wanda ake faɗin alherin sa ba zucci da baki kamar shi.
Wannan ne ya sanya Maudu’in wannan rubutu ya karkata kan tsakanin Marigayi Umaru Yar’adua da halinsa wane aka fi so?

Dalilin wannan Maudu’i shi ne Izma’in ra’ayoyi mabambamta sun nuna dole akwai dalili ɗayan-biyu da ya sa sunan Marigayi shugaban bai kwaranye ba kamar wasu kafinsa da kuma bayansa dama wasu da ke raye a halin yanzu amma tauraronsu ya dishe koma a ce ya ɓace kamar an yi khusufi.
Da ni da duk wanda ya bibiyi yarda taron addu’ar tunawa da wannan shugaba ya gudana a wannan shekarar zai lura da karuwar shigar masu faɗa-aji a fagen mulki da siyasa da ma masu tunanin nan, da bahaushe ke cewa ‘kowa ya tuna bara, bai ji daɗin bana ba’ ta fuskar canjin rayuwa.
Taken da aka yi wa kundin da aka gabatar wato ‘Abinda Yar’adua ya faɗa mani kuma ya koyar dani’ wanda ɗaya daga cikin yaransa na siyasa a Katsina, Dr. Muttaqa Rabe Darma ya wallafa na buƙatar duk wanda ya ci karo da wannan rubutu ya yi nazari kafin zagayowar irin wannan rana ta baɗi.
Yakubu Lawal
Ɗan Jarida ne Sannan
Jami’in Hulda da Jama’a
