November 17, 2026

Yaƙi Ya Ci Mutanen Arewacin Nijeriya…

images (5)

 

Daga Aliyu Abdullahi Malumfashi

 

A satin da ya gabata ne aka gudanar da taron masu ruwa da tsaki na hukumar raya yankin arewa maso yamma.

 

Jihohi dai sun kunshi Kano da Kaduna da Katsina da Zamfara da Kebbi da Sakkwato da kuma Jigawa.

 

Sai dai abin baƙin ciki da takaici shine yadda wani gwamna da jihar sa ke fama da matsalolin tsaro da na tattalin arziki tare da koma baya ya kauracewa wannan taro.

 

Kazalika ‘yan majalisun jihar ma ba su halarci wannan taro ba, fuskokin da aka gani su ne da jami’ar hukumar raya yankin arewa maso yamma

 

Haka kuma sarakuna da malamai da masana duk sun kauracewa wannan muhimmin taro da zai iya amfanar da yankin arewa maso yamma

 

Da yake an ce abin mamaki baya karewa, dai gashi takwarar wannan hukuma da ke kudu wato South East development commission sun yi irin wannan taro abin gwanin birgewa.

 

Hatta mataimakin shugaban kasa ya halarci taron har sun fito da sabbin shirye-shiryen masu dogon zango na shekaru 50 masu zuwa

 

Sannan suna san shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya mahimmantar da ayyukan raya ƙasa har na dalar Amurka biliyan 10

 

Daman ance naka shi ke bayar da kai, ko an so ku an ki yanzu dai an bar ‘yan arewa da batun nuna goyon baya ga ‘yan takarkari (Endorsement) da kuma sharholiya da wasu gwamnoni ke yi.

‎

About The Author