November 18, 2026

Fim ɗin ‘Five Winners’ Sabon Darasi ne ga Rayuwar Matasa. -Jammaje 

IMG-20260208-WA0019

 

DAGA MUKHTAR YAKUBU 

 

An bayyana sabon shirin ‘Five Winners’ Wanda a ‘yan kwanakin nan aka kammala zangon farko na ɗaukar sa a matsayin wani fim da ya zo da wani sabon salo na koyar da matasa darasin rayuwa musamman ma dai ga masu sha’awar yin karatu da kuma kishin dogaro da kan su.

 

Malam Kabiru Musa Jammaje ne ya sanar da hakan a lokacin tattaunawar su da wakilin mu inda yake bayyana manufar Fim din na ‘Five Winners’ a dandalin ɗaukar fim ɗin da aka gudanar a farfajiyar gidan namun daji da ke Kano wato Gidan Zoo.

 

 

Malam Kabiru Musa Jammaje wanda fitaccen Malamin turanci ne kuma Furodusa da ya shirya finafinai masu yawa da harshen turanci a Kannywood, ya ce aikin yana tafiya yadda ya kamata, kuma jarumai suna kokarin bayar da abin da ake so domin suna bin labarin yadda ya dace.

 

Malam Kabiru ya ƙara da su kan su ‘yan Kannywood suke mamakin yadda hakan ta kasance a cikin tsari da kwanciyar hankali.

 

Domin da yawan jaruman wadanda suka samu horo ne a makarantar Jammaje Academy bangaren koyar da aktin.”

 

Ya ƙara da cewa”Duk da ban taba yin fim mai dogon zango ba sai wannan gaskiya ni kaina abin ya burge ni domin ko a yanzu na samu darasi domin kowanne aiki akwai nasara da kuma kalubale”

 

Dangane da labarin kuwa Jammaje ya ce “labari ne mai kyau wanda mutane idan suka kalla za su samu ilimi a ciki, domin mun zo da wani sabon tsari da babu irin sa a Kannywood, kuma daman ba wai alfahari ba kamfanin Jammaje Production ya yi suna wajen samar da finafinai masu inganci tun a baya.

 

Kazalika ya ce shi wannan gasa ce aka shirya a tsakanin wasu ɗalibai a kan kimiyya da Adabi turanci da Hausa.

 

 

Don haka wannan fim din idan sun kammala za su baiwa gidajen talabijin sannan kuma za su saka shi a You Tube ɗin su mai suna Kabiri Musa Jammaje wanda hakan zai baiwa kowa damar ya kalla.”

About The Author