September 17, 2026

Yadda Shugabannin KAFIGAN Reshen Jihar Kano Suka Karɓi Rantsuwar Kama Aiki 

IMG-20260112-WA0003

 

 

Daga Mukhtar Yakubu 

 

An rantsar da sabbin shugabannin kungiyar ‘Yan fim ta KAFIGAN reshen Jihar Kano waɗanda za su jagoranci ƙungiyar na tsawon shekaru huɗu masu zuwa.

 

 

A ranar asabar 10 ga Janairun 2026 ne aka yi taron rantsar da sabbin shugabannin a ɗakin taro na Meenat Event Center dake Lodge Road a Unguwar Nassarawa G.R.A cikin garin Kano.

 

 

Taron wanda ya samu halartar dimbin jama’a daga sassa daban-daban na ƙasar nan an fara shi ne da misalin karfe 7 na dare.

 

 

Tun da farko da yake jawabi a wajen taron, shugaban kwamitin amintattu na kungiyar. Alhaji Ismaila Na’abba Afakallahu ya nuna farin cikinsa a game da yadda ‘yan fim suka karbi tafiyar wannan kungiya wadda a ɗan lokaci daga kafa ta zuwa yanzu an fara ganin ci gaba a game da yadda tafiyar take.

 

A cewar sa abu ne da ya kamata su yi godiya ga Allah bisa nasarorin da suke samu, kuma suna matukar godiya da haɗin kai da suke samu, kuma in sha Allahu a matsayin su na shugabanni za mu ci gaba da tsayin daka don ganin an cimma nasarar da ake buƙata ta kafa kungiyar.

 

Sai dai a nasa jawabin ɗaya daga cikin jagororin tafiyar na ƙasa. Alhaji Adamu Bello Ability ya bayyana sabuwar kungiyar ‘Yan fim ta ‘Kannywood Film Industry Guilds Associations ‘(KAFIGAN) a matsayin wata kungiya da ta zo domin ta kawo gyara a cikin masana’antar finafinai ta Kannywood.

 

 

In da yake cewa “Wannan kungiyar ‘Yan fim ce wadda ta haɗa kowa da kowa, kama daga Furodusa Darakta jarumai da sauran masu sana’a a cikin masana’antar Kannywood. Don haka wannan kungiya ba ta ware kowa ba, wajen tafiyar ta kowa nata ne.”

 

 

Ya ƙara da cewa ” Babbar manufar wannan yunkuri shi ne samar da daidaito da kuma haɗin kai a tsakanin mutanen da suke cikin masana’antar Kannywood da kuma hada ƙarfi waje guda domin tunkarar irin matsalolin da muke ciki, don haka za mu yi duk mai yiwuwa wajen ganin wannan masana’anta tamu ta samu ci gaban da ake bukata.

 

Adamu Bello Ability ya ƙara da cewa an fara sharewa na baya hanya ta yadda idan suka zo za su ci moriyar ta. Suna fatan waɗannan shugabanni da za a rantsar na reshen jihar Kano za su yi aikin tukuru wajen haɗa kai tare da jawo sauran abokan sana’ar su cikin wannan tafiya domin a gudu tare a tsira tare.”

 

Bayan kammala jawabin nasa ne aka rantsar da sabbin shugabannin, wadanda suka hada da Isah A Isah a matsayin shugaba.Mansurah Isah mataimakiya ta daya, Hannatu Bashir mataimakiya ta II, Sani Ahmad Kankarofi Sakatare da Muhammad Mukhtar Daneji (Tantiri) a matsayin jami’in yada labarai.

 

 

Sauran shugabannin sun haɗa da Shu’aibu Idris Lilisco da Muhammad A Bashir da Hafsat Abduhadi Tage da Mustapha Sharif da Anwar Abdulhadi Nasidi da Alin Baba da Hadiza Musa Maikano da Aminu Ilu Shehu Danbazau da Shehu Umar da Ibrahim Bala da Muhammad Sa’id Dalha Dandano, da kuma Habibu Yaro Haruna.

 

 

A lokacin da yake jawabi bayan rantsar da su a matsayin shugabanni. Sabon shugaban reshen jihar Kano, Alhaji Isah A Isah, ya yi alƙawarin tafiyar da kungiyar bisa gaskiya da riƙon amana, inda ya yi kira da abokan tafiyarsa da aka rantsar da su da su ba shi goyon bayan da ya kamata domin sauke nauyin da aka ɗora musu.

 

 

Haka nan ya yi kira ga masu gudanar da harkokin sana’o’in su a cikin masana’antar finafinai ta Kannywood da su rungumi wannan tafiyar, domin ta su ce gaba ɗaya don haka ya nemi gudummawar wajen tafiyar da kungiyar don a tafi tare a tsira tare..

About The Author