September 18, 2026

KAFIGAN Zata Kaddamar Da Sabbin Shugabanninta Reshen Kano

FB_IMG_1767882749202

DAGA MUKHTAR YAKUBU 

 

Sabuwar kungiyar masu shirya fim ta ƙasa ‘Kannywood Film Industry Guilds Associations’ (KAFIGAN) reshen Jihar Kano za ta ƙaddamar da shugabannin ta da za su tafiyar da shugabancin kungiyar a ranar asabar mai zuwa

 

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na kungiyar Mahamoud Tantiria ya sanyawa hannu aka rabawa manema labarai a Kano

 

Kwamitin ya shaida cewar, za a yi taron ƙaddamarwar ne a ranar Asabar 10 ga Janairun 2026 a ɗakin taro na Meenat Event Center da ke Lodge Road a Unguwar Nassarawa G.R.A cikin garin Kano da misalin karfe 5 na yamma.

 

Shugabannin kungiyar ta (KAFIGAN) reshen Jihar Kano da za a ƙaddamar karkashin Jarumi Isah A Isah a matsayin shugaba, Mansurah Isah a matsayin mataimakiya, Sani Ahmad Kankarofi Sakatare ,da Muhammad Mukhtar Daneji (Tantiri) a matsayin Jami’in yaɗa labarai.

 

Kungiyar Kannywood Film Industry Guilds Associations dai wata sabuwar Kungiyar ‘yan fim ce da take da muradin kawo gyara a harkar fim da kuma bunƙasa masana’antar ta hanyar kulla alaƙa da Manyan kamfanonin cikin gida da na waje domin ganin masana’antar ta samu damar yin gogayya da sauran takwarorin ta na cikin gida da na waje.

 

Ana sa ran dai mutane da dama za su halarci wajen taron na ƙaddamar da shugabannin idan Allah ya kaimu ranar.

About The Author