Tallafin Nuhu Ribadu: Yadda Musa Maisana’a Ya Raba Abinci Da Kuɗi ga Jaruman Kannywood
Popular News January 21, 2026
DAGA MUKHTAR YAKUBU
Fitaccen Jarumi a masana’antar Kannywood Musa Abdullahi, wanda aka fi sani da Maisana’a ya shiryi wani taro na rabon buhunnan shinkafa da kuɗaɗai ga wasu daga cikin jaruman Kannywood da suke cikin buƙatar taimako ta ɓangaren rayuwar yau da kullum.
A wajen taron dai an ga fuskokin tsofaffin jarumai masu yawa da suka halarci taron irin su Malam Kabiru Nakwango da Isa Bello Ja da Jazuli Kazaza da Lubabatu Madaki da sauran su.
Da yake jawabi a game da rabon abinci da kuɗin tallafi ga ‘yan fim din, Musa Maisana’a ya ce “Ita wannan rayuwa yadda take, komai a wajen Allah yake.don haka komai sai da yardar sa ake yi.
A cewar sa wannan abin da ka ga an yi wani sako ne daga wajen Malam Nuhu Ribadu mai baiwa shugaban ƙasa shawara a kan harkokin tsaro duba ga yadda ya ga ‘yan fim da ma duk wani da zai bada gudunmawa to a shirye yake da ya bada tallafi don a baiwa jama’a a matsayin gudummawa domin ya ji dadin gudanar da rayuwar sa cikin aminci.
Maisana’a ya nuna bukatar a wayar wa da mutane kai, a game da abin da ya shafi harkar tsaro, domin harkar tsaro ta kowa da kowa ce.
Don haka duk wani da ya ga wani abu da zai cutar da al’umma to ya yi maza ya kai rahoton ga ofishin Nuhu Ribadu ya sanar.
Haka kuma ya kara da cewa ba kuma ana nufin a tafi Abuja ba don kai rahoton, a a ofishin ‘yan sanda mafi kusa da kai nan ne ofishin Nuhu Ribadu. Don haka duk wani da ya ga wani abu da zai cutar da al’umma zai hanzarta ya je ya sanar.
Kazalika Musa Maisana’a ya ce za a bada gudunmawa yadda za a dakile abin da zai cutar da al’umma nan take.
“Wannan ya sa ake bayar da ‘gudummawa ga wanda ake ganin za su shiga gaba wajen wayar da kan al’umma, don haka wannan aikin ya shafi kowa da kowa ne har da kai domin a haɗu a wayar wa da mutane kai, wannan ba siyasa ba ce.” Inji shi
Ko a cikin Unguwar ku, ko a kan hanya akwai waɗanda za ka samu suna wani abu na cutar da al’umma, kuma ana taron a zo a sanar da iyayen yaran ga matsalar yaran su ko a sanar da hukuma.
To wannan ya sa al’umma suke ta cutuwa, dole ne sai al’umma sun fito, ko ɗanka ne ko ɗan wane idan ka ga zai cutar da al’umma ka fito ka wayar da kan al’umma a kan cewa wannan mai laifi ne, ko da ta ƙarƙashin ƙasa ne ka kai shi wajen hukuma, to ka taimaki jama’ar gari “
Dangane da yadda aka tsara rabon ga ‘yan fim kuwa cewa ya yi ” Ai shi wannan rabon na kowa da kowa ne, su ‘yan fim da ka ga an fara da su. To su abokan gwagwarmaya ne kuma su ne idon da jama’a suke kallo, don haka Muryar su za ta yi amo wajen kira ga jama’a da su sanar da hukuma idan sun ga wani abu da zai cutar da su.
Kuma da yake kashi na farko ne da muka fara, a yanzu mun samar da tallafi na mutane 50, kowane ya samu babban buhun shinkafa da Naira dubu hamsin.
Sannan kamar yadda ya faɗa wannan farko ne za a ci gaba da yi nan gaba. Muna fatan wannan abin ya ɗore a yi ta yi har tsawon rayuwar mu.
Jarumin finafinan Hausa ya bayyana cewa mutane ba su san muhimmancin ciyarwa ba. Ko da mutum ba zai iya sayen buhun shinkafa ba idan ka sayi ruwa leda ɗaya ka ajiye a kofar gidan ka idan an dawo daga masallaci duk wanda zai wuce ya ɗauka ya sha, to za ka ga sakamako.
Amma dai wannan da muke yi kuma za mu ci gaba da yi. To daga ofishin Nuhu Ribadu ne kuma mun zaɓi mu bayar ga tsofaffin ‘yan fim ne saboda a matsayin su na Dattawa da waɗanda su ake kallo ake raga wa harkar kuma suna da karfin fada a ji da za su wayar wa da mutane kai a game da harkokin tsaro da kuma muhimmancin zaman lafiya.” Inji Maisana’a
