Shirin AGILE Abu Ne Mai Kyau — Shugaban GDSS Funtua.
Shugabannin makarantun sikandiren Dukke da Funtua sun bayyana shirin tallafawa da kuma ilimantar da yaya mata a matsayin abu mai kyau.
Sun bayyana cewa shirin zai taimaka wurin magance wasu daga cikin matsalolin da ilimin makarantun sikandiren ke fuskanta a jihar nan, inji majiyar Popular News Hausa.
Abubakar Yaro da Lawal Rayyanu sun fadi hakan ne jim kadan bayan duba wasu ayyuka da aka gudanar karkashin shirin a makarantun su.
A makarantar Government Senior Secondary School, shugaban makarantar Abubakar Yaro ya ce gwamnatin jihar Katsina ce ta amince da yin ayyuka 3.
Ayyukan dai sun haɗa da gyaran ban-daki, gyaran rukunin azuzuwa 3 da kuma samar ma makarantar baki daya ruwa.
A makarantar Government Day Secondary School Funtua, shugaban makarantar Lawal Rayyanu ya ce yanzu haka ana cikin gyaran rukunin azuzuwa 4, tona rijiyar burtsatse da kuma sanya tankin ruwa domin samar da ruwa a makarantar.
Saboda suka yaba ma bankin duniya da gwamnatin jihar Katsina.
