September 17, 2026

Idan Katsinawa Suka Zaɓi Dakta Dikko Raɗɗa Ba Za Su Yi Da-Na-Sani Ba, Cewar Kwararren Masanin Tattalin Arzikin Ƙasa, Ibrahim Tukur Jiƙamshi

0

Kwararren masanin tattalin arzikin Ƙasa Da Kananan Masana’antun Kuma Shugaban Hukumar Zuba Jari Ta Jihar Katsina, Alhaji Ibrahim Tukur Jiƙamshi ya yi kira ga al’ummar jihar Katsina da su fito kwansu da kwarkwatarsu su zazzaga wa ɗan kakarar jam’iyyar APC a jihar Katsina, Dakta Dikko Umar Radda kuri’unsu don ganin ya samu nasarar lashe zaɓen gwamnan jihar Katsina a 2023.

Yace idan suka yi haka ba za su taɓa yin da-na-sani ba saboda gogewarsa a fannoni daban-daban da kuma tarin Ilimin boko da na addini da yake da shi da kuma hangen nesa.

Alhaji Ibrahim Tukur Jiƙamshi ya bayyana haka jim kaɗan bayan kammala wata ganawa ta musamman da dan takarar gwamnan jihar Katsina a karƙashin jam’iyyar APC, Dakta Dikko Umar Radda a Ofishin yakin neman zaɓensa dake cikin garin Katsina a ranar Alhamis da ta gabata.

Shugaban Hukumar Kula Da Haɓɓska zuba Jari Ta Jihar Katsina, Alhaji Ibrahim Tukur Jiƙamshi ya ƙara da cewa a wannan zaɓe mai karatowa na 2023, al’ummar jihar idan suka dubi kafatanin ‘yan takarar gwamnan jihar Katsina a jam’iyyu mabanbanta yana da wahalar gaske a samu nagartaccen ɗan takarar kamar Dakta Dikko Umar Raɗɗa.

Haka kuma ya bayyana al’ummar Najeriya gaba ɗaya sun amfana da irin ƙyakkyawan shugabancinsa na yadda ya riƙe Hukumar Kula Da ƙanana Da Matsakaitan Masana’antun Ta Najeriya da kuma irin sauye-sauye da ya kawo a Hukumar cikin shekara biyar.

Alhaji Ibrahim Tukur Jiƙamshi ya cigaba da cewa jihar Katsina na buƙatar matashin dattijo irin Dakta Dikko Umar Radda saboda irin baiwa da basira da kokarin ganin ya inganta rayuwar al’umma musamman matasa da kuma ƙananan Masana’antun wanda ya ke da gogewa akan fannin.

Alhaji Ibrahim Tukur Jiƙamshi ya ce “Ina da tabbacin zai kawo sauye-sauye masu ma’ana da za su inganta rayuwar al’umma jihar Katsina.”

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *