Gwamnan Bauchi Zai Mayar Da Kudaden Fom Ga ‘Yan takarar PDP Da Suka Fadi Zaben Fidda Gwani.
Gwamna Bala Mohammed zai mayarwa da duk wasu ‘yan takarar jam’iyyar PDP da suka sha kaye ko kuma suka fice daga zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP na baya-bayan nan a wani bangare na kokarin sasanta ‘ya’yan jam’iyyar. Kuɗaɗen da za a maido su ne abinda yan takarar suka kashe lokacin da suka sayi fom, inji majiyar Popular News Hausa ta jaridar
Gwamnan ya yi amannar cewa matakin zai tabbatar da hada babbar tawagar da za ta kai ga samun nasarar jam’iyyar a jihar da kuma kasa a zaben 2023.
Gwamna Mohammed ya bayyana hakan ne a lokacin da ya gana da daukacin ‘yan takarar jam’iyyar PDP a a gidan gwamnatin jihar Bauchi.
Gwamnan ya kuma yi alkawarin dawo da masu rike da mukaman siyasa da suka yi murabus daga mukamansu a gwamnatin shi da suka kasa cin tikitin jam’iyyar a lokacin zaben fidda gwani na jam’iyar PDP da aka kammala.
Da yake jawabi a madadin jam’iyyar, shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Hamza Akuyam, ya nemi afuwar ‘ya’yan jam’iyyar da suka fusata, ya kuma bukace su da su haɗa kai don samun nasarar jam’iyyar.
Idan dai za a iya tunawa Gwamna Bala Mohammed ya karbi rahoton kwamitin sulhu wanda ya ba da shawarar a mayar wa duk masu neman takara a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP domin samun nasarar jam’iyyar.
