September 16, 2026

An Kama Yan Sanda 7 Bisa Zargin Amsar Na Goro A jihar Edo.

0

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama wasu ‘yan sanda bakwai bisa zargin cin hanci da rashawa a wani mataki na wanke rundunar ‘yan sandan jihar Edo daga munanan abubuwa.

Bayanin wannan matakin da kwamishinan ‘yan sandan jihar Abutu Yaro ya dauka na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakiyar jami’in hulda da jama’a na rundunar‘yan sandan Jennifer Iwegbu ta rabawa manema labarai a karshen makon nan, inji majiyar jaridar Popular News Hausa ta AIT.

A cewar sanarwar, an tsare jami’an yan sandan bakwai da aka kama, kuma an kafa kwamitin wucin gadi domin gudanar da bincike a kan zargin cin hancin da rashawa da ake yi masu.

Kwamitin na karkashin jagorancin Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda ma sashen ayyuka James Chu mai lambar waya 08035511263 da kuma shugaban kwalejin su, Avanrenren Godwin mai lambar waya 08058813590, a matsayin Mataimakin Shugaban kwamitin.

Sanarwar ta kara da bayyana bukatar ganin kwamitin ya binciki wasu jami’an ‘yan sanda da wani faifan bidiyo na kwanan nan ke nunawa a shafin Twitter inda wani kurtun dan sanda mai suna Victor Osabuohien ke amsar na-goro hannun wani mai abun hawa Architect Bolu.

Sauran jami’an ‘yan sandan da aka kama kan zargin cin hanci da rashawar kuma suke jiran ladaftarwa sun hada da:

  1. AP/No 135192 ASP Godspower Ijebu
  2. AP/No 199776 Inspector Ebatamole Philip
  3. AP/No 271855 Inspector Ademola Benjamin
  4. AP/No 271825 Inspector Inaite Vincent
  5. AP/No 271897 Inspector Robert Esikise
  6. AP/No 200713 Inspector Adefaye Samuel.

Yaro a yayin da yake yaba kokarin ganin an fahimci ‘yan sanda, ya kuma bukaci al’ummar jihar Edo da suka hada da wadanda aka tatsi kudin cin hanci hannun su da su yi amfani da lambobin wayar da aka tanadar ta hanyar da ta dace domin mika korafe-korafensu da sazu taimaka wa kwamitin wajen gudanar da ayyukan bincike da kuma yin adalci a kan laifukan.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *