September 17, 2026

JAMB Ta Ce Dalibai 40,000 Ne Suka Rubuta Jarabawar Da Basu Yi Ba.

0

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da sikandire ta JAMB ta ce sama da dalibai 40,000 ne sake rubuta Jarabawar da basu samu yi ba a wannan shekarar.

Jarabawar dai ta gudana ne a cibiyoyi 45 dake fadin Najeriya jiya Asabar.

Shugaban hukumar JAMB din na Najeriya Farfesa Ishaq Olayede ne ya bayyana hakan ga manema labarai a lokacin da yake duba jarabawar a Lagos, inji majiyar Popular News Hausa.

Ya ce an shirya jarabawar ne don amfanin ɗaliban da basu samu damar rubuta wadda aka yi a cikin watan Mayu ba.

Hakan dai ya faru saboda dalilai da dama, da suka hada dana maguɗin jarabawa.

Hukumar ta yi nuni da cewa, tana yin bitar rohotonni da kuma bidiyon da Camera sirri ke naɗa bayan an kammala jarabawa.

Ta ce wasu kwararru ne ke gudanar da irin wannan ayyuka na naɗar mata bayanai da nufin gano ayyukan saba doka.

Sauran daliban da suka tsinci kan su cikin wannan jarabawar sun haɗa da masu matsala lokacin ɗaukar zanen hannu, masu matsalar katin dan kasa, da dai sauran su.

Ya kuma koka kan batun samun wasu cibiyoyi dake taimakawa dalibai ayi maguɗin jarabawa a lokacin jarabawar farko da aka yi a cikin watan Mayu.

Kamar yadda shugaban hukumar JAMB din ya bayyana, wannan jarabawa da aka sake rubutawa ta lashe ma hukumar tsabar kudin Najeriya sama da miliyan 100.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *