Ba Kudi Muke So Gwamnatin Tarayya Taba Mu Ba — ASUU.
Kungiyar malam Jami’o’in Najeriya (ASUU) ta zargi gwamnatin tarayya da fadi ma yan Najeriya wani abu daban sabanin zahirin bukatun su.
Kungiyar ta ce ba ta taɓa samun matsala da gwamnatin da ta shuɗe ba a cikin batun tattaunawar su, inji majiya Popular News Hausa.
Shugaban kungiyar ASUUn Najeriya Professor Emmanuel Osodeke ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke maida ma ƙaramin ministan kwadagon Najeriya Festus Keyamo martani kan maganar da ya yi ta cewa gwamnatin tarayya ba za ta ciyo bashi ba don kawo karshen yajin aikin na tsawon watanni 5.
Ya ce tatsuniya ce maganar da Keyamo ya yi ta cewa ASUU na bukatar trillion 1.1 domin kawo karshen yajin aikin.
Ya bukaci gwamnatin tarayya da ta daina ruɗa yan Najeriya da wani zance na daban.
Ya ce kungiyar ASUU ba ta bukatar kudi, kawai dai tana bukatar gwamnatin Najeriya ta inganta jami’o’in kasar don ganin sun birge dalibai masu zuwa daga ƙasashen duniya.
Shugaban kungiyar ASUUn ya kara da cewa, ya zama dole malaman jami’a su samu albashi mai tsoka da zai sa malamai daga ƙasashen duniya su iya zuwa su koya a jami’o’in kasar.
Farfesa Emmanuel Osodeke ya ce ba wata tattaunawa mai dadi tsakanin su da Gwamnatin Najeriyar.
Kamar yadda ya bayyana, gwamnatin tarayya ta amince da zuba jimullar kudi naira trillion 1.4 a jami’o’in gwamnatin tarayya dana jihohi tun a shekarar 2013 bayan da kungiyar ta koka mummunan halin da jami’o’in suke ciki.
Ya ce a cikin shekarar 2013 ne gwamnatin tarayyar zata bada naira miliyan 200,000, sannan ta ci gaba da bada naira miliyan 220,000 a kowace shekara har tsawon shekaru 5 masu zuwa.
Amma bayan bada kason farko na kudin, ba a sake jin wani labari ba.
