Yadda Taron APC A Gyara Ya Gudana A Yankin Daura Ta Jihar Katsina
Shugaban tafiyar APC a gyara na jihar Katsina Yusuf PSP ya bayyana cewa sun gudanar da baban taro a shiyyar Daura a jihar Katsina.
Ita dai APc a gyara wasu matasan jam’iyyar APC ne suka kafa wanda kuma ake yi wa wani kallon ‘yan tawaye, amma dai sun faɗa cewa suna son a kawo gyara ne a jam’iyyar APC.
Haka kuma kungiyar ta ƙaddamar da shuwagabannin ta na yankin Daura da suka da ƙananan hukumomi 12 na yankin domin tattauna yadda tafiyar zata cigaba.
Ƙananan hukumomin da aka ƙaddamar da shuwagabannin sun haɗa da Kankia, Kusada da ingawa da Mashi da Dutsi, da
Bindawa da Mani, da Daura, Sandamu da Mai’adua, Da Ɓaure da kuma Zango
Kwamared PSP ya ƙara da cewa sun samu gagarumar nasara a zaman su na yankin Daura duba da irin halin da jam’iyyar su ta APC ta shiga ajihar Katsina
“Abubuwan da taron ya kunsa sun haɗa da tattaunawa akan batun yadda shuwagabannin jam’iyyar APC a matakin jiha da ƙananan hukumomi da kuma mazaɓu za su gyara kuskuren da suke ganin anyi domin tunkarar zaɓe mai zuwa” inji shi
Haka kuma ya ƙara da cewa ba sun yi taron bane domin cin mutuncin wani ko wasu ba, sun yi ne domin a kawo gyara a wuraren da suke ganin ba a yi daidai ba a tafiyar jam’iyyar APC a jihar Katsina.
Kwamared Yusuf PSP wannan tafiya ta su tafiya ce ta kowa da kowa saboda duk wanda ke kishin jami’yyar APC to ya zo a gyara domin samun nasarar cin zaɓe mai zuwa.
Ita dai wannan ƙungiya an kafa ta domin jan hankalin da kira ga shuwagabannin na jam’iyyar APC da su yi kokarin wajen cika alkawarin da aka ɗauka tun shekarar 2015 .
Sai dai wannan ƙungiya ta APC a gyara na fuskantar matsin lamba daga wasu ɓangarori na jam’iyyar APC tare da faɗin cewa wasu ne ke ɗaukar nauyin ta.
