September 18, 2026

Rawar Da ‘Yan Jarida Ya Kamata Su Taka Wajan Samar Da Zaman Lafiya A Rahotanninsu – IMC

0

Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina

Kungiyar Interfaith Mediation Centre (IMC) ta bayyana irin rawar da ‘yan jarida da kafafen yaɗa labarai ya kamata su taka a lokacin gudanar da aiki su a jihar Katsina da ke fama da hare-haren’yan bindiga ba dare ba rana.

Haka dai na zuwa ne a lokacin wani taro tsakanin jagororin IMC da kuma ‘yan jarida masu aikawa da rahotanni daga jihar Katsina domin lalubu hanyoyin da za su taimaka wajan wanzar da zaman lafiya a sha’anin tsaro.

Tun da farko da yake gabatar da jawabi kodinatan kungiyar Malam Hayatu Nura ya fara ne da cewa an zabi wasu daga cikin ‘yan jarida domin su bada ta su gudunmawa wajan wayar da kan jama’a akan muhimmancin zaman lafiya a jihar Katsina da ƙasa baki ɗaya.

Ya ƙara da cewa wannan shirin ana gudanar da shi ne ƙarƙashin shirin inganta zaman lafiya a cikin al’umma (community initiatives to promate peace) domin tattauna mahimman batutuwan da suke faruwa a cikin al’ummomin da ke fuskantar hare
-haren ‘yan bindiga

” Ta hanyar irin wannan tattaunawa ne zamu iya gano abubuwa da ke haifar da rashin fahimta a tsakanin al’ummomi da addinai da haddasa rikici tare da lalubu hanyoyin da za a warware su ta hanyar wayar da kan jama’a a ilimance” inji shi

Haka kuma wannan taro zai bada damar tattaunawa tsakanin ‘yan jarida da jami’an kungiyar domin fuskantar abinda zai iya zama maslaha ta hanyar sanya kishi da zaman lafiya a cikin rahotannin su na Yau da kullum.

Bayan doguwar tattaunawa tsakanin mahalarta taron da suka haɗa da ‘yan jarida da jami’an kungiyar IMC da wakilan kungiyar an cimma matsaya akan abubuwa da dama da suka haɗa da;

Na farko ana son ‘yan jarida su riƙa tunawa da batun zaman lafiya a cikin rahotannin su na yau da kullum, da kaiwa hukumomi tsaro ziyara domin ƙara samun haɗin kai don ayi aiki tare cikin nasara.

Haka kuma an cimma matsayar cewa ita kungiyar IMC ta karfafa shigowar mata cikin wannan tafiya domin bada ta su gudunmawa wajan wanzar da zaman lafiya sannan a shigo da hukumar hana da sha fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA)

Akwai batutuwa da dama da aka tattaunawa wanda dukkansu an bada mahimmanci akan batun wanzar da zaman lafiya a tsakanin al’ummomi ta hanyar lura da abubuwa da ke faruwa na hare-haren’yan bindiga da sauran batutuwa da suka shafi al’umma.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *