September 18, 2026

Wata Majiya Na Cewa, Hukumar EFCC Na Yin Aikin Sirri A Wurin Taron APC.

0

Wata majiya mai karfi a cikin hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta tabbatar da cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa a halin yanzu tana gudanar da wani bincike a boye domin lura da yadda wakilai ke tada zaune tsaye da kuma sayen kuri’u a zaben fidda gwani na shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki.

Majiyar mai tushe data tabbatar da hakan ga wakilin jaridar PUNCH, ta ce, “A yanzu haka suna filin taron jam’iyyar APC suna gudanar da wani aiki a boye.

Muna sa ido kan ayyukan, kuma muna sa ido sosai kan abubuwan da suka faru na jawo wakilai, sayen kuri’u, da sauran ayyukan zabuka ko na kudi da ka iya faruwa.”

Majiyar ta kuma tabbatarwa da jaridar ta PUNCH cewa, hukumar ta yaki da cin hanci da rashawa na gudanar da aikin a boye domin kamo masu aikata laifin ba tare da sun sani ba.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke nuna makudan kudi kimanin dalar Amurka 40,000 ne manyan ‘yan takara suka zuba a zaben fidda gwani na shugaban kasar dake gudana.

A dai dai kwanaki 10 da suka gabata ne jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, wasu jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC sun kai farmaki babban filin wasa na Moshood Kashimawo Abiola dake Abuja a lokacin da ake gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa na babbar jam’iyyar adawa ta PDP.

Jami’an sun isa wurin ne da misalin karfe 4:40 na yamma.

Jaridar PUNCH ta kuma ruwaito cewa, jami’an sun mamaye wurin da aka gudanar da zaben fidda gwanin na shugaban kasa na jam’iyyar PDP ne a Abuja biyo bayan rahotannin zargin sayen kuri’u da kuma ba wakilai cin hanci a wurin taron.

Hukumar EFCC, wacce ke tabbatar da rahoton jaridar PUNCH, daga baya ta fitar da wata sanarwa a hukumance, inda ta bayyana cewa jami’anta sun kutsa kai wajen taron ne domin sanya ido kan yadda wakilai ke tafka kura-kurai da kuma tafka magudi.

“Jami’an sun kasance a wurin zaben fidda gwanin na shugaban kasa na jam’iyyar PDP a filin wasa na MKO Abiola don sanya ido a kan aikin, musamman ma don duba yadda wakilai ke jawowa da kuma wasu matsalolin kudi.” Inji wani bangaren sanarwar.

Da wakilin jaridar PUNCH ya tuntubi jami’in hulda da jama’a na hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, sai ya ki cewa komai kan lamarin.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *