Gwamna Raɗɗa Ya Kaddamar da Aikin hanyoyi 20 Masu Fitilun da ke Amfani da Hasken Rana a Malumfashi
Gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umar Raɗɗa ta ƙaddamar da aikin fara hanyoyi 20 masu tsawon kilo mita 10.7 da za a yi tare sanya a fililu masu amfani da hasken rana a garin Malumfashi.
Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da aikin hanyar gwamna Dikko Umar Raɗɗa ya ce aikin zai lakume kimanin naira biliyan 10.2 wanda ya bayyana a matsayin babban zuba jari wajen bunƙasa sufuri da tattalin arziki da kuma dama wajen samar da aikin yi tare da kyautata rayuwar al’umma.
“Wannan aiki ya wuce gina hanyoyin kawai, ya nuna dubarun zuba jari da al’umma za ta amfana da shi nan gaba wajen sauƙaƙa sufuri da kasuwanci tare da samar da muhali yaya yadda cigaba mai kyau zai tabbata” inji Raɗɗa.
Gwamna Raɗɗa ya ce samar hanyoyin zai taimaka matuƙa gaya wajen sauƙaka isa ga cibiyoyin kiwon lafiya da ilimi da inganta harkar tsaro da suka haɗa wasu alummomi tare da samar yin kasuwanci.
A cewar sa, ayyukan hanyoyi a Malumfashi na ɗaya daga cikin kudirin wannan gwamnati na faɗaɗa birane da ƙawata su a fadin jihar Katsina domin tabbatar da an samu daidaito a fannin cigaba.
Kamar yadda ya bayyana hanyoyi za su rage tsawon tafiya da kuma saukin cunkoso sannan su bayar da kariya ga al’umma, da kasuwanni da makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya sannan fitilun kan hanya da za a saka za su taimaka wajen bunƙasa tsaro da tsawaita lokutan kasuwanci tare da karfafa zirga-zirga a cikin garuruwa.
Haka kuma gwamnan ya ƙara da cewa wannan aikin hanyar zai bunƙasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi ga matasa sannan ya tallafi ƙananan yan kasuwa sannan ya karawa dukiya daraja.
Daga ƙarshe ya yabawa ma’aikatar ayyuka ta jihar Katsina saboda yadda ta nuna jajircewa sannan ya yi kira ga kamfanin Mother Cat da za su gudanar da aikin da su yi aiki mai inganci sannan su kammala cikin lokaci.
Sannan gwamnan ya yi kira ga al’umma da su kasance masu bada haɗin kai domin a samu nasarar da ake bukata.
Tunda farko da yake jawabi Kwamishinan ayyuka da jihar Katsina injiniya Sani Magaji ya ce aikin zai ƙara fito da irin jajircewar gwamnatin Malam Dikko Umar Raɗɗa akan ayyukan raya ƙasa da tattalin arziki.
