Yadda Ministan Gidaje Da Masari Suka Halarci Ƙaddamar da Littafin “Jagora Abin Koyi”
Ministan Gidaje da Raya Birane, Engr. Muttaƙa Rabe Darma PhD, ya halarci bikin ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar Sheikh Imam Abdulwahab Hassan mai taken “Jagora Abin Koyi.” Bikin ya haɗa manyan baƙi daga sassa daban-daban domin karrama gudunmawar malamin ga ilimi da addini.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Harkokin Siyasa, Alhaji Ibrahim Kabir Masari, tare da sauran manyan jami’an gwamnati, malamai da masu ruwa da tsaki.
Jiga-jigan gwamnati da ƴan siyasar da suka halarci taron sun yaba da irin gudunmawar da Sheikh Imam Abdulwahab Hassan ya bayar wajen yaɗa ilimi da tarbiyya.
An bayyana cewa littafin “Jagora Abin Koyi” ya yi bayani kan rayuwa, gwagwarmaya da irin gudummawar da Sheikh Imam Abdulwahab Hassan ya bayar ga al’umma, tare da fatan zai zama abin koyi anan gaba.
