September 18, 2026

Gwamnatin Jihar Katsina Na Goyon Bayan Shirin Farfaɗo da Abinci Mai Gina Jiki Da Kiwon Lafiyar Mata. -Gwamna Raɗɗa 

IMG-20260702-WA0011

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bayyana cewa gwamnatin sa na goyon bayan shirin farfaɗo da abinci mai gina jiki tare da kula da lafiyar mata masu juna biyu na CGPP

 

Haka kuma ya ƙara da cewa wannan haɗin gwiwar ya yi daidai da kudirin gwamnatin sa na inganta harkokin kiwon lafiyar mata da ƙananan yara a matakin farko

 

Malam Dikko Raɗɗa ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake karɓar bakuncin tawagar shirin “Core Group Partner Project’ (CGPP) wanda suka ziyarci shi a fadar gwamnatin jihar Katsina

 

A cewar sa, zuba jari a fannin abinci mai gina jiki da ingantacciyar kiwon lafiya na da matuƙar mahimmanci wajen rage mace-macen mata masu juna biyu da jarirai tare da samar da samar da al’umma masu koshin lafiya

 

Ya kuma tabbatar wa ƙungiyar cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da haɗa hannu da ita wajen tallafa wa shirye-shiryen kiwon lafiya na al’umma, yaƙin wayar da kai, da matakan da za su taimaka wajen magance matsalar ƙarancin abinci mai gina jiki.

 

A jawabin sa, jami’i mai kula da shirin core group partner project a jihar Katsina Abubakar Ahmed ya bayyana jin daɗin sa da irin matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka akan batun abinci mai gina jiki

 

Haka kuma ya bayyana shirinta na ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da gwamnatin jihar domin faɗaɗa ayyukan inganta abinci mai gina jiki, kula da lafiyar mata, da sauran shirye-shiryen kiwon lafiyar al’umma, musamman ga masu buƙata.

About The Author