November 17, 2026

Gwamna Raɗɗa zai kafa kotun da zata hukunta masu cin zarafin mata da ƙananan yara a Katsina 

IMG-20260702-WA0011

 

Gwamnatin jihar Katsina Ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umar Raɗɗa zata kafa wata kotu ta musamman zata hukunta masu ɗabi’ar cin zarafin mata da ƙananan yara a fadin jihar.

 

Gwamnan yana magana ne a lokacin da tawagar wayar da kan al’umma akan cin zarafin mata da ƙananan yara ta kai masa ziyara a ofishin sa.

 

Wannan ziyara na ƙarkashn kulawar mai ɗakin gwamnan jihar Katsina Hajiya Zulaihat Dikko Umar Raɗɗa.

 

Haka kuma gwamnan ya bayyana cewa mahimmancin wannan batu ya bada umarnin a gabatar da shirin wayar da kai a gaban majalisar zartarwa domin sakon ya isa ya nada ake so.

 

Ya ƙara da cewa cin zarafin mata da ƙananan yara a matsayin babbar matsalar zamantakewa da ke kawo raunana zuciya da tunanin mata da ƙananan yara.

 

Gwamna Raɗɗa yana mai jaddada cewa gwamnatin sa ba zata zura ido tana ganin ana cin zarafin mata da ƙananan yara ba, dole ne doka ta yi aikin ta.

 

Sai dai a nata jawabin uwargidan gwamnan jihar Katsina Hajiya Zulaihat Dikko Raɗɗa ta bayyana cewa cin zarafin mata da yara ba matsalar zamantakewa ba ce kaɗai, naƙasu ne ga cigaban shugabanci.

 

Ta ƙara da cewa akwai matuƙar buƙatar a sanya hannu akan batun da shafi shirye-shiryen kariya da karfafa dokoki da bunƙasa tattalin arziki mata ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da sarakunan gargajiya da malamai da kuma kungiyoyin fararan hula domin cimma nasara.

About The Author