September 19, 2026

Na Yaba Da Ƙoƙarin Mata Wajan Fitowa Kaɗa kuri’a Cewar Hadiza Bala Usman

0

Tsohuwar shugaban hukumar jiragen Ruwa kuma jigo a jam’iyyar APC Hajiya Hadiza Bala Usman ta yaba da ƙoƙarin mata wajan fitowa zaɓe domin suma a dama da su a harkokin siyasa

Hadiza Bala Usman ta yi wannan maganar ne jim kaɗan bayan ta kammala jefa kuri’ar ta Musawa firamare da ke garin musawa ta jihar Katsina

Haka kuma ta ce jajurcewar da mata da ke yi ya kamata shuwagabanni su ƙara gane irin gudunmawar da mata ke bayarwa a harkokin siyasa

Ta yi kira ga shuwagabannin da su riƙa duba gudunmawar da mata ke badawa wajan raba muƙamai, ba wai a ɗauki mukamai a baiwa waɗanda ba su bada gudunmawa ba.

Hajiya Hadiza ta ce yadda suka tattauna da jama’a ba su hakuri na azo ayi wannan tafiya, ta ce tana da ƙwarin gwiwar cewa suke da nasara daga sama har ƙasa.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *