Mutumin Da Ya Sha Kwata Don Taya Buhari Murna Ya Koma PDP Daga APC.
Aliyu Mohammed Sani ɗan Bauchi da ya sha tare da yin wanka da ruwan kwata don murnar nasarar Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis ya fito karara ya bayyana cewa ya janye biyayyarsa ga jam’iyyar APC mai mulki.
Sani da ake cema Ali Gayu ya ce ya yi nadamar abin da ya aikata domin an bar shi shi kadai ya mutu bayan faruwar lamarin.
A cewarsa, Alhaji Musa Azara na jam’iyyar PDP ne kawai ya damu da shi.
Ya ce, “Sunana Aliyu Mohammed Sani, wanda aka fi sani da Ali Gayu Na Baba Buhari, amma a da.
“Kusan kowa yana sane da cewa lokacin da Muhammadu Buhari ya ci zaben 2019, na yi wanka tare da shan kwata domin murnar nasarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu a zaben.
Muhammad Aliyu Sani ya kara da cewa; “Dalilin da ya sa na fice daga jam’iyyar APC shi ne, duk da rahotannin da aka rika yadawa kan matakin da na dauka a kafafen yada labarai, ba su damu da ni ba, a cewar majiyar Popular News Hausa ta jaridar Newtelegraph.
