September 18, 2026

Lokacin Da Ya Kamata Mutanen Kankia Su Gaji Da Ni, Lokacin Ma Suka Sabunta Sabuwar Soyayya Gareni. -Hon. Salisu Hamza Rimaye

0

Zaɓaɓɓen ɗan majalisar dokokin jihar Katsina mai wakiltar ƙaramar hukumar Kankia a jam’iyyar APC Hon. Salisu Hamza Rimaye ya bayyana irin soyayyar da mutanen Kankia ke yi masa musamman ba shi dama karo na uku a majalisar dokokin jihar Katsina

Hon. Salisu Hamza Rimaye ya bayyana hakan kwana ɗaya da bayyana shi a matsayin wanda ya sake lashe zaɓen dan majalisa karo na uku wanda kuma ba a taɓa samun wani ya yi sau biyu ba, amma shi ga shi ya samu karo na uku a ƙarƙashin jam’iyar APC.

Da yake mika godiyar sa bisa wannan karamci da mutanen Kankia suka yi masa ya ce tunda aka dawo mulkin dimokuraɗiyya shine mutun na farko da ya maimaita kujerar majalisar dokokin jihar Katsina sau uku, saboda haka yana godiya ga mutanen ƙaramar hukumar Kankia

Sannan Hon. Salisu Hamza Rimaye ya ce abinda zai ƙara tabbatarwa da mutanen Kankia shi ne, a baya bai taɓa ba su kunya ba, yanzu ma insha’Allahu ba zan ba su ba.

“Baban abinda ya burgeni ga mutanen Kankia shi ne daidai lokacin da ya kamata ace sun gaji da wakilci na, amma dai gashi sun ƙara sabunta sabuwar soyayya gareni.” Inji shi

A cewar sa baban sirrin faruwar haka bai wuce hakuri da juriya ba, saboda shi ɗan siyasa an san shi da juriya domin ya kai ga nasara da ake buƙata.

Ɗan Majalisar ya ce ƙaramar Hukumar Kankia jami’a ce ta siyasa, babu wanda ake yi wa wayo, kowa ana bashi damar sa, kuma ya ce ya tsarewa abokin takararsa da kuri’a 12,00 duk da cewa a wajan tattara sakamakon zaɓe an samu matsaloli a wasu runfunan guda 6

Hon. Ya ce yana da baban tanadin da ya yi wa mutanen Kankia, inda ya ce zai ninka ƙoƙarinsa wajan ganin ya samarwa mutanen Kankia romar dimokuraɗiyya a wannan karo fiye da lokacin baya.

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *