An Kama Alhassan Doguwa A Filin Jirgin Saman Kano.
‘Yan sanda sun kama shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan Najeriya Alhassan Ado Doguwa bisa zarginsa da hannu wajen kashe wasu mutane tare da kona sakatariyar jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a lokacin zaben da aka kammala.
Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da cewa akalla mutane uku ne suka mutu a lokacin da aka ƙona sakatariyar jam’iyyar NNPP da ke Tudunwada.
Mutane biyu ne suka kone kurmus a lokacin rikicin yayin tattara sakamakon zaben majalisar wakilai ta Doguwa/Tudunwada wanda a karshe aka bayyana Doguwa ya lashe zaben.
Wata majiya mai tushe daga cikin ‘yan sandan ta shaida wa wakilin jaridar dailytrust dake zama majiyar Popular News Hausa cewa, an kama Doguwa ne a filin jirgin saman Malam Aminu Kano a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa Abuja.
Majiyar ta ce rahoton da hukumar ‘yan sanda ta fitar a Tudunwada ya bayyana cewa Doguwa da kansa ya jagoranci ‘yan baranda da suka kona sakatariyar NNPP, inda akalla mutane biyu suka kone kurmus.
“Ya kuma yi amfani da bindigar dogarinsa domin yin harbi. Don haka mun kama shi da laifin kisa da kone-kone.”
“A halin yanzu yana sashen binciken manyan laifuka na hedkwata, kamar yadda majiyar da ta bukaci a sakaya sunanta dake wurin ta bayyana”
Kakakin rundunar ‘yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, bai amsa kiran wayar da aka yi mashi ba.
Tun da farko, Doguwa a wata zantawa da manema labarai, ya musanta zargin da ake masa, inda ya ce ya samu labarin cewa ‘yan sanda na neman sa, amma bai samu wata gayyata a hukumance ba.
Ya kuma musanta zargin cewa ya harbe mutane da dama a rikicin, yana mai cewa shi ba shi da bindiga, bai san yadda ake amfani da ita ba.
Sai dai ya ce rikicin ya faro ne lokacin da magoya bayan jam’iyyar NNPP suka ɓullo da tunanin kona ofishin INEC inda kuma magoya bayan jam’iyar APC suka fatattake su.
