An Sasanta Rikici Tsakanin Makiyaya Da Manoma A Guri Ta Jihar Jigawa
An sasanta Rikici tsakanin rikicin makiyaya da manoma na kasar Guri wanda ya samu halartar mai martaba sarkin Hadejia Alh. Adamu Abubakar Maje Wanda ya samu tarba daga Shugaban Karamar Hukumar Guri Alhaji Musa Shuaibu
Taron ya hada da makiyayan kasar Guri da manoma Wanda anyi Jan Hankali ga al’ummar kasar kan Zaman lafiya, malamai sun ja Hankali da harshen hausa, maganci da kuma fulatanci, anyi Kira da kuma Allah ya wanzar da Zaman lpy a kasar Guri da kasar mu Baki daya.
Babban limamin kasar Hadejia malam Yusuf abdurrahmad yayi Karin bayanin zaman lpy a kasa.
Daga bisani Mai martaba sarki yayi Kira ga hukuma ta saka ido akan Masu yawo da makami da kuma Masu sae da miyagun kwayoyi, ya Kara Kira ga hukuma cewar duk Wanda yayi laifi a hukunta shi Wala makiyayi ko manomi na kasar
Wakilan Manoma da makiyaya sun gamsu da bayanai Daga bakin shuwagannin mu sun kuma yi Godiya da kuma alkawarin wannan Abu ya zama tarihi a kasar nan insha’Allahu.
Jagoran wanzar da Zaman lpy kuma chief security na Karamar Hukumar Guri alhaji Musa Shuaibu Muh’d Guri yayi jawabin Godiya da addu’ar Allah Ubangiji ya sake wanzar da Zaman lpy a Kasan Guri Allah kuma ya maida kowa gidansa Lafiya.
