September 18, 2026

Gwamna Masari Ya Tallafawa Wadanda Harin ‘Yan Bindiga Ya Shafa A Garin Guga

0

Gwamnatin Jihar Katsina a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Bello Masari, ta bayar da tallafin kudi da Kayan abinci ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da wadanda suka samu raunuka a yayin harin Yan Bindiga na Garin Guga ta Karamar Hukumar Bakori.

Kwamishinan Wasanni Da Walwalar Jama’a Na Jihar Alhaji Sani Aliyu Danlami ne ya jagoranci wata tawwaga da ta mika tallafin a madadin Gwamna Aminu Masari.

Idan masu karatun The Fact 24 basu manta ba, a Ranar 7 ga watannan da muke ciki ne Yan Bindiga suka yi dirar Mujiya a Garin na Guga inda suka hallaka mutane 9 da raunata wasu da dama, tare da kone dukiya ta Miliyoyin nairori.

Kamar yadda Kwamishina Danlami ya bayyana, Gwamna Masari ya bayar da tallafin ne domin rage wasu daga cikin wahalhalunda wadanda lamarin ya Shafa suke fuskanta.

Tallafin dai ya hada da Kayan abinci da naira 100,000 da aka baiwa Iyalan wadanda suka rasa rasa rayukansu.

A dayan bangaren kuma,wadanda suka samu rauni, an baiwa kowannensu buhun shinkafa da buhun dawa da 50,000.

Bugu da kari, iyalan wadanda Yan ta’addar suka sace an basu tallafin Kayan abinci, inda wadanda aka kone ma gidaje da shaguna suma zasu karbi tallafin da zarar an Kammala kididdige su.

Sauran wadanda maganta sun hada da ,Dan Majalissar Dokoki da ke Wakiltar Karamar Hukumar Bakori Dr.Aminu Kurami da Mai Garin Guga.

Sun yabawa Gwamna Masari akan tallafawa wadanda lamarin ya Shafa.

The Fact 24

About The Author

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *