An tallafawa ƙananan ‘Yan Kasuwa 120 Da Jari A Ƙaramar Hukumar Giade jihar Bauchi.
An kaddamar da shirin tallafawa kananan yan kasuwa a karamar Hukumar Giade kimanin 120 da jari.
Yayin da Kwamishinan Al’adu Da Yawon Bude Ido Na Jahar Bauchi Hajiya Dr Asma’u Ahmed Giade (Hon Commissioner Culture And Tourism Bauchi State). Ta jagoranci shirin.
Shugaban Gamayyan Yan Kasuwa ba Jahar Bauchi Alhaji Abdallah Y Muhammad (MD Abdallah Caps Venture’s) shine jigo da karkashin sa aka zagulo wannan ƙananan ya kasuwa da aka fara tallafa ma masu ƙananan karfi domin kara musu karfin gwiwa kan sana’oi su cikin wannan Gwamnati na Sanata Bala Abdulkadir Muhammad wanda yake fatan kowa ya samu abinda zai dogara da kan sa.
Shugaban Gamayyar kungiyoyin yan kasuwa na jihar Bauchi Alh Abdallah Caps ya isa garin Giade ne tare da tawagar yan shugabannin kasuwa na.
Sabuwan Kasuwa Railway Da Zango Da Na Yan Gwari Na Muda Lawal Market Da Sauran Zababbun Masu Rike Da Mukamai Ciki Harda Shugaban Yan Kasuwa Na Karamar Hukumar Bauchi Alhaji Yunusa Abubakar Lk Wanda Shima Yana Daya Daga Cikin Wanda Sukayi Rakiya Wa Shugaban Gamayyan.
Taron Yasamu Halartan Manyan Baki Ciki Harda Shugaban Karamar Hukumar Giade Alhaji Usman Randy Shugaban Jami’yar P D P Na Karamar Hukumar Giade Da Kuma Hakimin Karamar Hukumar Giade.
Shugaban Yan Kasuwa Na Jahar Bauchi Abdallah Caps Yayi Jawabi Na Babban Bako A Wannan Guri Ya Yabawa Dr Asma’u Ahmed Giade Bisa Wannan Abun Alheri Da Tayi Wa Jama’an Yankinta Yayi Kira Da Saura Shuwagabanin Da Suyi Koyi Da Wannan Hazikar Mata.
Yayin da ake tsakiyar taron wani abun taba zuciya ya faru lokacin da aka fa rabon tallafin !!
Ana Cikin Tsakiyan Taro Sai Ga Daya Daga Cikin Mata Da Zasu Amfanan Da Wannan Tallafin Da’akayi Mai Suna maryam Babani faguji Giade Ankirata Sai Akaga Gurguwace Bata Da Kafa Shugaban Karamar Hukumar Giade Ya Tambaya Akace Ahanka Da Yaganta Tayi Karatun Primary Secondary Har Yanzu Matakin NCE Bata Bari Zuciyanta ya mutu Da Yawon Baraba.
Nan Take shugaban ƙaramar hukumar na Giade ya ce ya Dauketa Aikin Wucin Gadi Kuma Da Albashin 25,000 Duk Wata Yayi Alkawarin Ana Fara Daukan Ma’aikatanta Sunantane Nafarko A Cikin Wannan Karamar Hukumar Giade Lura Da Yadda Tarike Mutuncinta Da Na Iyayen ta Hakanne Yasa Yaji Tausayin ta.
Wannan abu yayi matikar burge mahalarta taron sun ji dadin Wannan Kokari Da Yayi Mutane Da Yawa Sun nuna farin cikin su da kuma yaba masa kan wannan abun alheri da yayi take Malam Zainab Baba Giade ta fashe da kuka a wurin na farin ciki kan abin da akayi mata na Alheri.
Take Shugaban Gamayyan Yan Kasuwa Na Jahar Bauchi Alhaji Abdallah Caps ya mika Godiya kan wannan abun alheri da akayi ma yar kasuwa mai karamin karfi kuma mai fama da lalura.
Shugaban yace irin wannan abu yana cikin abubuwan alheri da yafi kauna a rayuwan sa ko iya wannan abu da ya faru munci ribar zuwa Giade kuma an yi abun alheri da muke fatan Allah ya mana budi domin sa ya kara bude zuciyoyin shugabanni su ci gaba da tallafawa masu karamin karfi a zahiri ina cike da farin ciki maras misaltuwa inji Alha Abdallah Caps.
A karshe ya mika Godiya su ga Shugaban Karamar Hukumar Giade Hon Usman Randy tare kuma da masa addu’an alheri.
