Da Gaske ‘Yan Bindiga Sun Tashi Garin Bugaje?
Labaran da ke shigo mana yanzu shi ne wanda ake cewa ‘Yan bindiga sun tarwatsa garin Bugaje da ke cikin karamar hukumar jibiya ta jihar Katsina.
Wannan gari dai ya sha fama da haren-haran ‘yan bindiga tare da kashe mutane da kwashe dukiyiyonsu ba sai daya ba, ba sau biyu ba.
Aminu Bugaje ya rubuta a shafinsa na facebook inda yake nuna alhinin yadda ‘yan bindiga suka tashi garin su ba don Allah ba.
Inda ya kara da cewa yanzu garin mai tarin albarka ta mutane da kasar noma da kiwo amma a yanzu ba mutun ,ba dabba ba kayan abincin su, sai kangaye da tsuntsaye kanana.
Ya ce duk mai san tabbatar da abinda ya fada sai ya je garin Bugaje domin ganewa idonsa abinda yake fada gaskiya ko karya.
Daga karshe ya kare rubutun nasa da yin addu’a da cewa Ya Allah mun kai kukammu agareka🙏🙏🙏
Da tambayar da mafi yawan jama’a ke yi shi ne da gaske an tashi garin Bugaje ta hanyar korar mutanen garin zuwa wani wuri na daban?
haka kuma muna kokarin ji daga hukumomin tsaron domin tabbatar da wannan ikirari da Aminu Bugaje ya yi na cewa ‘yan ta’ada sun kori mutanen garin Bugaje
