‘Yan Bindiga Sun Sake Kashe Wani Dan Kasuwa A Katsina
Daga Maman Garin, Katsina
‘Yan Bindiga da ba a san yawan su ba sun sake kai wani hari a sabon garin Malam Yahuza da ke cikin karamar hukumar Batagarawa inda suka kashe mutum daya.
A daran jiya talata da misalin karfe 2:00 da dare suka shiga garin a saman mashina dauke da muggan makamai inda suka yi wa gidan wani dan kasuwa tsinke domin sace shi.
Majiyarmu ta shaida mana cewa bayan ‘yan bindigar sun shiga gidan Alhaji Abu Mai Bulawus sun kama shi suna kokarin tafiya da shi amma ya ki amincewa.
Ganin yadda ya ba su wahala kuma ya ki amincewa a tafi da shi ga kuma makwabtansa suna neman kawo masa dauki sai kawai suka yanke shawarar harbinsa.
Majiyarmu ta ce bayan sun harbeshi sun gudu ana ƙoƙarin kai shi asibiti ya ce ga garinku nan, sakamakon wannan harbi da suka yi masa.
Sabon garin Malam Yahuza yana kan hanya zuwa Batsari daga yammacin garin Katsina a cikin karamar Batagarawa sannan ‘yan bindiga na yawan kai masu haren-haran wuce gona da iri.
Sai dai kuma har zuwa lokacin hada wannan rahoto duk kokarin da muka yi domin ji daga hukumomin bai samu ba, amma dai da zaran sun maganto za a ji karin bayani
