Mun Dauki Karin Ma’aikata 90 Saboda Mu Kara Inganta Aikinmu -Shugaban DM Kurfi
Daga El-Zaharadeen Umar, Katsina
Tun da farko da yake bayyana makasudin daukar wadannan matasa aikin shugaban Kamfanin samar da hasken wutar lantarki mai kula da ofishin Sabon Layi, Katsina Alhaji Ashiru Mammam ya yi jan hakalin ga sabbin ma’aikatan da su kama aikin inda ya ce su zage damtse wajen gudanar da ayyukan na yau da kullin.
Ya bayyana cewa baban dalilin da yasa suka kara daukar wadanda maaikata shi ne yadda jamaa suka fahimci aikin KEDCO a baibaiye a can baya, amma yanzu suna san su kara inganta wannan aikin na su.
Alhaji Ashiru Maman ya ce lalai akwia kalubale a wannan aiki, mutun ya san cewa an dauki shi aiki an bashi amana saboda haka dole ne ya kula da ita wannan amana bakin gwargwado domin ya sauke hakkin da ya rataya akan sa.
Dangane da abokan hulda kuwa ya ce lallai jamaa su sa ido so sai, za su ga canji, ba kamar KEDCO din da suka sani ba ce a baya, yanzu abubuwa za su canza musamman batun bada wuta wanda ada ana samun karancinta yanzu kuma an samu wasu sauye-sauye.
Ina mai tabbatarwa da abokan huldarmu cewa za su rika samun wuta akalla awa 15 zuwa 20 a duk rana, saboda haka nake amfani da wannan damar in sanar da su cewa ya kamata suma a ga canji daga wajan musamman wajan biyan kudin wuta tunda dai ga ta an sameta inji shi
Shima a nasa jawabin ga manema labarai a lokacin wani dan kwarya-kwaryar bikin raba takardun shaidar kama aikin (Offers) shugaban kamfanin DM Karfi Hon. Danlami Kurfi ya yi dogon bayani akan dalilinsu na daukar matasa 90 aiki a wannan kamfani na su.
Dankami Kurfi wanda ya samu wakilicin daya daga cikin manajojin kamfanin, Nura Muhammd Kurfi ya ce sun cika alkawarin da suka dauka na cewa za su bunkasa wannan kamfani ta hanyar daukar karin ma’aikata domin yin aikin daidai da zamani.
Ya ce duba da yadda suke ganin halin da matasa suka shiga a wannan lokaci saboda rashin aiki yi, idan har suka shigo da su za a rage masu zaman kashe kwando kuma alumma za su amfana da su, sannan za su samu makoma mai kyau a rayuwarsu nan gaba.
Nura Muhammad Kurfi ya kara da cewa wannan shi ne karo na farko, kuma nan gaba kadan za a cigaba da daukar karin wasu maaikata domin ganin kwaliya ta biya kudin sabulu a wannan Kamfani da DM Kurfi.
A cikin watan janairu na wannan shekarar da mauke ciki ne, kamfanin DM Kurfe da KEDCO suka kulla wata yarjejeniyar kasuwanci wanda zai gudan a tsakanin su musamman kula da hanyar samar da wutar lantarki da ta shafi baban titin IBB da ke cikin garin Katsina da kuma wasu wurare.
Haka kuma kamfanin na DM Kurfi shi ke da alhakin da duk wata hidima da ta shafi kula da harkokin wuta na wannan yanki, inda shirin ya shafi amsar kudin wuta, kula da gyaran wuta, sanya wuta, da kuma yanke wuta ga wadanda ba su biyan kudin wuta, da amsar korafe, korafen al’umma na yau da kullin.
